Za mu yi wa Atiku da Obi ritaya ranar Asabar – Tinubu

Za mu yi wa Atiku da Obi ritaya ranar Asabar – Tinubu

A yau, Alhamis, ne jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewar a ranar Asabar mai zuwa ne za su yi wa Atiku ritaya domin hakan ne ma fi alheri ga Najeriya.

Ban taba boye abotar da ke tsakanin da Atiku ba. Abokina ne, kuma za mu cigaba da abota bayan mun yi ma sa ritay a ranar Asabar, 16 ga watan Fabarairu.

“Ranar Asabar za mu yi ma sa ritaya saboda hakan ne ma fi alheri ga Najeriya da shi kan sa Atiku.

“Watakila ma har Obi za mu yi wa ritaya tare da maigidan sa domin su koma gefe su koyi tausayin talaka,” a cewar Tinubu.

Tinubu ya bayyana cewar babu wani abun kirki da Najeriya za ta ci moriya a manufofin yakin neman zaben Atiku.

Za mu yi wa Atiku da Obi ritaya ranar Asabar – Tinubu

Atiku daTinubu
Source: UGC

Tinubu ya yi wadanan kalamai ne a cikin wani jawabi da mai yada labaran sa, Tunde Rahman, ya fitar.

Tsohon gwamnan na jihar Legas y ace Atiku ba zai iya bunkasa tattalin arzikn Najeriya ba saboda akidar sa irin ta ‘yan jari hujja ba.

Manufar mu da ta su ta banbanta, sabanin jam’iyyar PDP, mu, a APC mun yarda cewar arzikin Najeriya na dukkan ‘yan Najeriya ne ba na wasu tsiraru ba. Duk wani dan Najeriya na da ‘yancin samun damar yin arziki ta hanyar amfani da basirar sa ko sana’ar da su ke yi.

DUBA WANNAN: Dan takarar mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan Buhari, ya hakura da takara

“Bai kamata a raina talaka ko kaskantar da shi ba, saboda da gumin su aka gina tattalin arzikin Najeria.

“Manufar su ta inganta tattalin arzikin shine buda wa wasu ‘yan tsirarun abokai bakin aljihun asusun gwamnati don su kwashi dukiyar kasa yayin da talaka ke cigaba da shan bakar wuya.

“Saboda damuwar da APC ta yi da talaka ne ya sa ta kirkiri shirin tallafa wa talaka na N-Power, ciyar da dalibai a makarantu da bayar da tallafi ga kananan ‘yan kasuwa (Trader-Moni),” a cewar Tinubu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel