Zan shafe ta’addanci daga kasar nan idan har aka zabe ni a karo na biyu - Buhari

Zan shafe ta’addanci daga kasar nan idan har aka zabe ni a karo na biyu - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jadadda jajircewar gwamnatinsa wajen magance matsalolin ta’addanci da rashin tsaro da ke addaban kasar.

Buhari wanda ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga dandazon jama’ar da suka halarci gangamin kamfen dinsa a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu a jihar Katsina yayi alkawarin shafe ta’addanci daga kasar.

Shugaban kasar ya dauki alkawarin cewa idan har aka sake zabarsa a karo na biyu, zai yi duk iya bakin kokarinsa wajen ganin ya fitar da mutanen yankin arewa maso gabas baki daya daga kankin Boko Haram.

Zan shafe ta’addanci daga kasar nan idan har kuka zabe ni a karo na biyu - Buhari

Zan shafe ta’addanci daga kasar nan idan har kuka zabe ni a karo na biyu - Buhari
Source: UGC

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba noman shinkafa muhimmanci a kasar tare da kudirin gabbaka tsaron abinci.

Shugaban kasar ya bayyana cewa manomar shinkafa sun samu tallafi sosai daga gwamnatin nan don haka an rage shigo da shinkafa yar waje.

KU KARANTA KUMA: Buhari ba mutum bane mai tsananin son mulki – Inji Oshiomhole

Da fari shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bukaci mutanen Najeriya da na jihar Katsina da su fito kwansu da kwarkwata a ranar Asabar domin su zabi shugaba Buhari a karo na biyu.

Oshiomhole ya bayyana cewa Buhari ya cancanci sake shugabanci a karo na biyu saboda ya riki amanar da yan Najeriya suka bashi shekaru hudu da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel