Zaben 2019: Za'a kulle dukkan iyakokin Najeriya ranar Juma'a

Zaben 2019: Za'a kulle dukkan iyakokin Najeriya ranar Juma'a

Gabanin zaben 2019, hukumar shiga da ficen Najeriya NIS ta bada umurnin kulle dukkan iyakokin Najeriya da kasashen dake makwabtaka ranan Juma'a misalin karfe 12 na rana.

A wata jawabin da kakakin hukumar, Sunday James, ya saki kuma shugaban hukumar, Muhammad Babandede ya rattaba hannu, ba za'a bude iyakokin ba sai ranan Lahadi da karfe 12 na rana.

Jawabin yace: "Gwamnatin tarayya ta bada umurnin kulle dukkan iyakokin Najeriya daga karfe 12 na ranar Juma'a zuwa karfe 12 na ranar Lahadi, 24 ga watan Febrairu 2019.'"

"Za'ayi hakan ne domin hana shiga da fice yayinda ake gudanar a zabe saboda haka ana sanar da jama'a su sani."

Iyakokin da za'a kulle ya kunshi Nijar, Chadi, da Kamaru.

KU KARANTA: Ana saura kwana daya zabe, jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a garin Jos

A bangare guda, yan bindiga a ranan Alhamis sun kai mumunan hari kan wata motar hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC, a jihar Benue, yayinda ake raba kayayyakin zabe kananan hukumomi.

Kwamishanan hukumar INEC na jihar, Dr. Nentawe Yilwatda, ya bayyana hakan ne yayinda yake magana da manema labarai a jihar.

Yace motar na dauke da kayayyakin zabe irinsu alkaluman rubutu, kayayyakin jami'an zabe, huluna, akwatinan zabe da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel