Ana saura kwana daya zabe, jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a garin Jos

Ana saura kwana daya zabe, jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a garin Jos

Ana saura kwana daya kacal da zaben shugaban kasa ya majalisun tarayya, jigogin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, akalla dari biyu a jihar Plateau sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Mambobin sun bayyana cewa dalilin sa yasa suka fita daga PDP shine sun lura cewa jam'iyyar na kokarin saba alkawari da shirin da akayi na gudanar da mulki a jihar dui ga cewa dan takaranta gwamnan jihar, Sanata Jeremiah Useni, zai nemi tazarce ko ya lashe zaben 2019.

Wannan saba alkawari ne saboda daya daga cikin dalilan da yasa mambobin PDP suka zabi Jeremiah Useni a zaben fidda gwanin jihar shine don shekarunsa da kuma yarjejeniyar cewa shekara hudu kadai zai yi.

Amma uwar jam'iyyar ta musanta wannan zargi da mambobi sukeyi, ta ce kawai suna fakewa ne da guzuma su harbi karsana da kuma kokarin bata PDP.

Mai magana da yawun wadanda suka sauya shekan, Garba Abubakar, wanda yayi jawabi a taron yakin neman zaben APC a karamar hukumar Mangu na jihar inda yace abinda yasa suke tare da PDP a baya shine alkawarin Jeremiah Useni cewa shekaru hudu kasai zai yi.

KU KARANTA: Hotuna da Bidiyo: Yadda Buhari ya karkare yakin neman zabensa na 2019

A bangare guda, jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewar a ranar Asabar mai zuwa ne za su yi wa Atiku ritaya domin hakan ne ma fi alheri ga Najeriya.

“Ban taba boye abotar da ke tsakanin da Atiku ba. Abokina ne, kuma za mu cigaba da abota bayan mun yi ma sa ritay a ranar Asabar, 16 ga watan Fabarairu.

“Ranar Asabar za mu yi ma sa ritaya saboda hakan ne ma fi alheri ga Najeriya da shi kan sa Atiku.

“Watakila ma har Obi za mu yi wa ritaya tare da maigidan sa domin su koma gefe su koyi tausayin talaka,” a cewar Tinubu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel