Zaben 2019: Atiku ya bukaci mutanen Adamawa da su zabe shi

Zaben 2019: Atiku ya bukaci mutanen Adamawa da su zabe shi

Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP), a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu ya kammala rangajin kamfen dinsa a Adamawa, inda yayi kira ga mutanen jihar da su marawa dan jiharsu baya sannan su fito su zabe shi.

Yace a matsayinsa na dan su, ba sai yayi kamfen a gida ba, amma sai dai zai bukaci iyayensa da kada su bashi kunya a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

Atiku ya jadadda cewa zai magance matsalolin rashin tsaro, rashin aiki, talaucio da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta.

Zaben 2019: Atiku ya bukaci mutanen Adamawa da su zabe shi

Zaben 2019: Atiku ya bukaci mutanen Adamawa da su zabe shi
Source: UGC

A nashi jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Mista Uche Secondus ya bukaci mutanen Adamawa da su tabbatar da son da suke yiwa Atiku da jam’iyyar inda ya kara da cewa dansu ne dan takarar da ya cancanci inganta Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Za mu durkusar da arzikin Najeriya muddin Buhari ya lashe zabe – Tsagerun Niger Delta

Secondus ya kuma bukaci hukumar INEC, hukumomin tsaro da dukkanin masu ruwa da tsaki da su tabbatar da anyi zabe na gaskiya.

A nashi bangaren dan takarar kujerar gwamnan Adamawa a jam’iyyar PDP, Alhaji Umaru Fintiri, yace idan har aka zabe shi a matsayin gwamna zai tabbatar da ilimi kyauta sannan ya wajabta shi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel