Dan takarar mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan Buhari, ya hakura da takara

Dan takarar mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan Buhari, ya hakura da takara

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar GDPN, Alhaji Ibrahim Modibbo, ya yi watsi da takarar sa tare da bayyana goyon bayan sa ga takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ja’iyyar APC.

Da ya ke bayyana goyon bayan na sa ga shugaba Buhari ranar Talata a Abuja, Modibbo ya ce kwazon shugaban da jam’iyyar sa a cikin shekaru uku ne babban dalilin da ya sa shi ya yanke wannan shawara.

Modibbo ya ce shugaba Buhari na da kyakyawar manufa ga Najerya da mutanen ta tare da yin kira ga jama’a da su fito kwai da kwarkwata ranar Asabar domin zazzaga wa Buhari kuri’un da za su bashi damar zarce wa a kan karagar mulkin Najeriya a karo na biyu.

Dan takarar ya kara da cewa a baya Najeriya ta sha wahala a hannun ‘yan tsirarun mutane marasa kishi da ba sa kaunar cigaban talaka.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan Buhari, ya hakura da takara

Dan takarar mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan Buhari
Source: UGC

A cewar sa, a kaf fadin Afrika ta yamma, ba a taba samun wani shugaban kasa da ya yaki cin hanci da rashawa kamar yadda shugaba Buhari ya yi a cikin shekaru hudu da ya yi a kan mulki ba.

Ya bayyana cewar sake zaben Buhari zai kawo karshen talauci da rashin zaman lafiya da ya dabaibaye Najeriya.

DUBA WANNAN: Kamfen: Katsinawa sun yi wa Buhari kara, hotuna

Kwazon Buhari a cikin shekara uku ya isa tabbacin cewar zai kawo abubuwa ma su kyau da su ka zarce na baya, musamman a bangaren noma da inganta tattalin arziki.

“Na yanke shawarar goya ma sa baya saboda aiyukan alheri da ya ke yi, akwai bukatar na goya ma sa baya domin ya cigaba,” a cewar Modibbo.

Da ya ke karbar Modibbo da magoya bayan sa, shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari mai kula da matasa da mata, Buba Marwa, yay aba ma sa bisa yanke shawara mara wa Buhari baya tare da bashi tabbacin cewar sake zaben Buhari zai zama alheri ga Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel