Dalilin da yasa Atiku bai kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Ogun ba - Daniel

Dalilin da yasa Atiku bai kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Ogun ba - Daniel

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel ya ce rashin isashen lokaci ne ya hana dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar samun daman kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Ogun.

Daniel, wanda shine mataimakin shugaban kamfen din Atiku na yankin Kudu ne ya jagoranci jirgin yakin neman zaben Atiku a mazabun Ogun ta Tsakiya da Yamma gabanin babban zaben.

Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku bai kaddamar da yakin neman zabensa a jihar ta Ogun ba amma matarsa, Mrs Titi Abubakar ta ziyarci jihar domin yi masa kamfen din.

Dalilin da yasa Atiku bai yi kamfen a jihar Ogun ba

Dalilin da yasa Atiku bai yi kamfen a jihar Ogun ba
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

A wata hira da Daniel ya yi da manema labarai a jiya, ya jadada cewa 'jihar Ogun ai ta Atiku ce' shi yasa ba sai ya tafi jihar domin kaddamar da yakin neman zabe da kansa ba.

Ya ce: "Atiku ya ziyarci jihar Ogun sau da yawa a baya. Abin sai da tsari. Wani lokaci ana bukatar babban taro wasu lokutan kuma ba a bukatar hakan. Kuma kun san yadda jihar Ogun ta ke. Ina tsammanin mun kammala abinda ya da ce muyi.

"Misali a shekaran jiya da, ya kamata ya tafi Abuja amma muka soke ziyarsa saboda akwai karancin lokaci. Daya daga cikin dalilin mu shine mun tabbatar mutanen Ogun Atiku suke so. Anyi an gama."

Tsohon gwamnan ya shawarci 'yan Najeriya kada su amince da duk wani abu mai alaka da magudin zabe saboda hakan ne ya jefa Najeriya cikin mawuyacin hali.

Ya kuma ce dan takarar shugabancin kasa na PDP ya nuna alamar cewa yana da sha'wa da niyyar 'sauya tsarin rabon kasa a Najeriya.'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel