Soyayya: Wani mutum a Jos ya yi hijira zuwa wurin zabe don kada wa Buhari kuri'a (Hotuna)

Soyayya: Wani mutum a Jos ya yi hijira zuwa wurin zabe don kada wa Buhari kuri'a (Hotuna)

- Wani dattijo a jihar Filato, Abubakar Shettima ya baro gidansa ya tare a wurin zabe saboda yana son ya zama mutum na farko da zai jefawa Shugaba Buhari kuri'a

- Shettima ya ce yana son ya zabi Shugaba Muhammadu Buhari ne a matsayin tukwuici saboda ceto su da ya yi daga hannun hukuma bayan kama shi da akayi a 2015

- A halin yanzu dai Shettimaya riga ya yi kwana guda a wurin zaben inda daga shi sai dardumar sallah da Al-kur'ani da kuma katin zabensa

Wani mazaunin garin Duala a Dogon Dutse da ke karamar hukumar Jos ta Arewa mai suna Abubakar Shettima ya yi hijira daga gidansa zuwa wurin kada kuri'a a Dogon Agogo inda ya ke zaune cikin shiri domin zaben shugaban kasa da za ayi ranar Asabar.

Soyayya: Mutane a Jos sun fara hijira zuwa wurin zabe don kada wa Buhari kuri'a

Soyayya: Mutane a Jos sun fara hijira zuwa wurin zabe don kada wa Buhari kuri'a
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben 2019: INEC ta fitar da jerin laifukan zabe 15

Shettima mai shekaru 59 a duniya ya ce yana son ya zama mutum na farko da zai jefawa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari kuri'a a matsayin tukwuici saboda sakinsa da akayi bayan an kama shi a shekarar 2015 inda ake zarginsa da alaka da kungiyar Boko Haram.

Bayan ya baro gidansa a safiyar ranar Laraba, Shettima ya ce ya riga ya kwana guda a wurin zaben kuma zai sake kwanaki biyu a wurin domin ya samu damar kada kuri'ansa.

Soyayya: Mutane a Jos sun fara hijira zuwa wurin zabe don kada wa Buhari kuri'a

Soyayya: Mutane a Jos sun fara hijira zuwa wurin zabe don kada wa Buhari kuri'a
Source: Twitter

"Tuni na tura mata ta jihar Borno tun safiyar ranar Alhamis domin tayi zabe kuma ina da yara uku da shekarunsu ya isa na zabe.

"Biyu daga cikinsu suna Jos kuma za su zabi Buhari yayin da guda daya mace tana Maiduguri tare da mijinta saboda haka sai abinda mijinta ya yanke shawara tayi," inji shi.

Shettima samu wuri ya zauna a kan dardumarsa ta salla rike da Al-Kur'ani mai girma a hannunsa da kuma katin zabensa a aljihunsa.

Shettima ya magantu a kan yadda aka kama shi tare da wasu mutane a tashar mota a Jos sannan aka kai su Bauchi, Yobe da Jihar Borno duk a cikin mummunan hali har sai da gwamnatin Shugaba Buhari ta karbi mulki sannan aka sake su bayan an gudanar da bincike an gano ba su da alaka da 'yan ta'addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel