2019: Matukar za a yi zabe na gaskiya Atiku zai yi nasara - Business Day

2019: Matukar za a yi zabe na gaskiya Atiku zai yi nasara - Business Day

Yayin da gobe Juma'a za ta kasance jajiberin zaben 2019 wanda za a gudanar a ranar Asabar, 16, ga watan Fabrairu, masu ruwa da tsaki daga duk wani lungu da sako na duniya na ci gaba da bayyana ra'ayoyin su gami da hasashe.

Wani babban kamfanin jarida na Business Day da ke da tushen sa a jihar Legas, ya bayyana ra'ayin sa gami da hasashen yadda sakamakon zaben jibi Asabar zai kasance tsakanin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, da kuma dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Cikin wallafar ta a ranar Talata 12, ga watan Fabrairu, jaridar Business Day ta ruwaito cewa, matukar za a gudanar da tsarkakken zabe na gaskiya da adalci, to kuwa ba bu shakka dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP zai yi nasara da kaso 56.5 cikin 100 na adadin kuri'un al'ummar kasar nan.

2019: Matukar za a yi zabe na gaskiya Atiku zai yi nasara - Business Day

2019: Matukar za a yi zabe na gaskiya Atiku zai yi nasara - Business Day
Source: Facebook

Duba da hasashe na yiwuwar rashin adalci, binciken jaridar Business Day ya hikaito yadda Buhari zai yi nasara sakamakon wasu dalilai da suka rinjayar ma sa da riba gami da fa'idoji ta fuskar kujerar iko da ya ke rike da ita a halin yanzu.

Dalilai da jaridar ta wassafa sun hadar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC da ita kanta ke karkashin kulawa da iko na shugaba Buhari. Akwai kuma hukumomin tsaro na 'yan sanda, DSS, rundunar dakarun soji da ke karkashin jagoranci na shugaban kasa.

KARANTA KUMA: 2019: Tsagerun Neja Delta sun yiwa kudirin Atiku mubaya'a

Doriya akan wannan dalilai, jaridar Business Day ta na kuma zargin manyan makarraban shugaban kasa Buhari da suka hadar da Mamman Daura, Abba Kyari da sauran su akan hankoro na sai inda karfin su ya kare wajen ci gaba da rike akalar jagorancin kasar nan.

Hasashen babban kamfanin jaridar ya tabbatar da cewa, sabanin wannan manyan dalilai da ta wassafa, ba bu wata dama da Buhari ya ke da ita wajen cin galaba akan babban abokin adawar sa da ya kasance Atiku.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel