Da dumi-dumi: Yan bindiga sanya da kayan Sojoji sun tare motar dake dauke da kayan zabe

Da dumi-dumi: Yan bindiga sanya da kayan Sojoji sun tare motar dake dauke da kayan zabe

Labarin dake shigowa da dumi-dumi na nuna cewa wasu yan bindiga a ranan Alhamis sun kai mumunan hari kan wata motar hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC, a jihar Benue, yayinda ake raba kayayyakin zabe kananan hukumomi.

Kwamishanan hukumar INEC na jihar, Dr. Nentawe Yilwatda, ya bayyana hakan ne yayinda yake magana da manema labarai a jihar.

Yace motar na dauke da kayayyakin zabe irinsu alkaluman rubutu, kayayyakin jami'an zabe, huluna, akwatinan zabe da sauransu.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya karkare yakin neman zabensa na 2019

Yace: "Wannan gaskiya ne, an kaiwa motarmu hari yayinda ake safarar kayayyakin aiki a unguwar Logo kuma wasu mutane ne sanye da kayan sojoji."

Mun kawo muku cewa a ranan Litinin 11 ga watan Fabrairu ne Rundunar Sojin Saman Najeriya NAF ta fara taimakawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC jigilar kayayakin zaben ta zuwa wasu jihohin Najeriya domin gudanar da zaben 2019.

Legit.ng ta gano cewa za a gudanar da jigilar kayayakin zaben da rana da kuma cikin dare inda za ayi amfani da jirgin NAF C-130 Hercules da ke tashi daga filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikwe da ke Legas zuwa jihohin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel