Za mu durkusar da arzikin Najeriya muddin Buhari ya lashe zabe – Tsagerun Niger Delta

Za mu durkusar da arzikin Najeriya muddin Buhari ya lashe zabe – Tsagerun Niger Delta

- Tsagerun Niger Delta sun yi barazanar durkusar da tattalin arzikin Najeriya idan har aka sake zaben Buhari a matsayin shugaban kasa a karo na biyu

- ‘Yan tawayen sun ce, suna fatan kawo karshen mulkin Buhari ta hanyar zabar babban mai adawa da shi na jam’iyyar PDP

- A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa

Tsagerun Niger Delta sun yi barazanar durkusar da tattalin arzikin Najeriya idan har aka sake zaben shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu a zaben 2ransabar, 16 ga watan Fabrairu.

‘Yan bindigan sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu kasa da sa’oi’i 42 a gudanar da zaben shugabancin kasar.

Za mu durkusar da arzikin Najeriya muddin Buhari ya lashe zabe – Tsagerun Niger Delta

Za mu durkusar da arzikin Najeriya muddin Buhari ya lashe zabe – Tsagerun Niger Delta
Source: Depositphotos

‘Yan tawayen sun ce, suna fatan kawo karshen mulkin Buhari ta hanyar zabar babban mai adawa da shi na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da suka ce suna goyon baya.

Mayakan Niger Delta Avengers sun taka rawa a wasu rikice-rikicen da suka taimaka wa wajen tsindimar Najeriya cikin matsalar koma-bayan tattalin arziki a shekarar 2016.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka ya kira Buhari ta wayar tarho

A wani lamari na daban, Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnan jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, na neman lamuni da yarjewar sa akan yiwa Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, gwaji na taɓin hankali.

Yayin yakin zaben sa da ya gudanar cikin birnin Fatakwal, Wike cikin jawaban sa ga magoya baya ya yi kira na neman sahalewar shugaban Najeriya wajen yiwa Minista Amaechi gwaji na tabbatar da cikakkiyar lafiyar kwakwalwar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel