Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka ya kira Buhari ta wayar tarho

Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka ya kira Buhari ta wayar tarho

Tsohon shugaban kasar Amurka da bai samu damar yin ziyarar da ya shirya kaiwa Najeriya ba, Bill Clinton ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wayar tarho, inda suka kwashe tsawon mintoci suna tattauna batutuwan da suka shafi zaben ranar Asabar.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 14 ga watan Feburairu, inda yace shugaba Bill Clinton ya kira Buhari ne a daren Laraba, kuma ya bayyana rashin dadinsa na rashin samun damar kawo ziyarar da yayi niyya Najeriya.

KU KARANTA: Umarnin kama tsohon Alkalin Alkalai: Onnoghen ya ruga gaban kotu neman mafaka

Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka ya kira Buhari ta wayar tarho

Buhari da Clinton
Source: UGC

Babban makasudin ziyarar da Bill Clinton Najeriya shine domin halartar taron rattafa hannun yan takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019 akan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin shiga zaben da zai gudana a ranar 16 ga wata.

Sai dai duk rashin halartar Bill Clinton, taron rattafa hannun ya gudana a karkashin jagorancin shugaban kwamitin zaman lafiya ta Najeriya, tsohon shugaban kasa Abdul Salami Abubakar, kuma manyan yan takarar shugabancin Najeriya kamar Buhari da Atiku da sauransu duk sun hallara.

Shima shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ma Bill Clinton manufarsa ta tabbatar da an gudanar da zaben gaskiya da gaskiya a wannan karo, sa’annan ya bayyana Clinton a matsayin abokin arzikin Najeriya wanda ke kokarin ganin kasar ta zauna lafiya da kuma cigaban dimukradiyya.

Daga karshe Bill Clinton ya yi ma Najeriya da yan Najeriya fatan alheri yayin da suka gab da shiga babban zabn 2019 a ranar Asabar zuwa ranar 2 ga watan Maris, inda yayi kira ga yan Najeriya dasu gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel