Yan kasuwan kasashen waje sun zuba jarin dala biliyan 16.8 a kasuwanci a Najeriya

Yan kasuwan kasashen waje sun zuba jarin dala biliyan 16.8 a kasuwanci a Najeriya

Hukumar tattara alkalumma da kididdiga, NBS, ta bayyana adadin hannun jarin da yan kasuwan kasashen waje suka zuba a Najeriya ya karu matuka a shekarar 2018, fiye da abinda aka samu a shekarar 2017, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a shekarar 2018 kadai yan kasuwa sun antaya naira biliyan goma sha shida da miliyan tamanin da daya, wanda ya haura gwamman tiriliyoyi idan aka mayar da shi zuwa naira, yayin da a 2017 kuma aka samu dala biliuan 12.22.

KU KARANTA: Umarnin kama tsohon Alkalin Alkalai: Onnoghen ya ruga gaban kotu neman mafaka

Hukumar ta bayyana haka ne a yayin bayar da bahasin bayanai na karshen kashi na hudu na shekarar 2018 a shafinta na yanar gizo, sai dai tace an dan samu tsaiko a kashi na hudu na shekarar, inda aka shigo da jarin dala biliyan 2.14 kacal.

An bayyana jarin da yan kasashen waje ke shigowa dashi a matsayin kudaden kai tsaye da suka shigowa dasu don kafa kamfanoni, kudaden sayen hannayen jari a kamfanoni da kuma sauran hanyoyi zuba jari.

Kaso mafi tsoka na jarin da yan kasuwan kasashe waje suka zuba a Najeriya ya fito ne daga cinikayya tsakanin bankuna wanda akafi sani a turance ‘Portfolio Investment’, wanda ya samar da dala biliyan 11.80.

Bayanan da hukumar NBS ta fitar sun nuna kasar Birtaniya ce kan gaba wajen zuba jari a Najeriya, inda yan kasuwanta suka antaya dala biliyan 6.01 a kasuwanci a Najeriya, wanda hakan ya kai kashi 35.74 na jarin da suka shigo Najeriya a 2018.

Kasa ta biyu itace kasar Amurka, wanda take da dala biliyan 3.57 a kasuwannin Najeriya, Afirka ta kudu ce kasa ta uku dake da dala biliyan 1.15, kamar yadda NBS ta hakaito daga rahoto da babban bankin Najeriya ta fitar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel