Zabe: IG ya bayar da umurnin takaita zirga-zirgan ababen hawa

Zabe: IG ya bayar da umurnin takaita zirga-zirgan ababen hawa

Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya bayar da umurnin a takaita zirga-zirgan ababen hawa a ranar zabe. Mutane za su iya zirga-zirga da ababen hawansu ne daga karfe shida na safiya zuwa shida na yamma.

Hakan zai bawa 'yan sandan da sauran hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu na samar da tsaro da kuma hana bata gari yin katsalandan cikin zaben.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ACP Frank Mba a yau Alhamis a birnin tarayya, Abuja.

Zabe: IG ya bayar da umurnin takaita zirga-zirgan ababen hawa

Zabe: IG ya bayar da umurnin takaita zirga-zirgan ababen hawa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kungiyar Tijjaniya tayi karin haske a kan goyon bayan takarar Buhari

Sanarwar ta ce: "Domin tabbatar da tsaron kasa da lafiyar al'umma a ranar zabe na 16 ga watan Fabrairu, Sufeta Janar na 'yan sanda, IGP Muhammed Adamu ya bayar da umurnin takaita zirga-zirgan motoci daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yammacin ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun 2019.

"IGP din ya ce wannan zai taimakawa hukumomin tsaro wurin gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma tare da hana bata gari kawo cikas ga zabe."

Kazalika, Shugaban 'yan sandan ya tabbatarwa al'umma cewa an samar da isashen tsaro saboda haka kowa ya fita domin ya kada kuri'ansa ba tare da fargaba ko tsoro ba.

IGP din ya bawa mutane hakuri a kan matsin da wannan dokar za ta haifar kuma ya yi gargagin cewa rundunar za ta magance duk wani da aka samu yana kokarin saba dokokin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel