Duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’a za mu biya shi lada – EFCC

Duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’a za mu biya shi lada – EFCC

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa za ta biya lada ga duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’u a zaben

- Ya ce wannan tsari na daga cikin tsarin busa usur din fallasa masu harkallar kudade da EFCC ta shigo da shi

- A ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu ne dai za a fara zaben shugaban kasa da na yan majalisar dokoki

A kokarin da hukumomin kasar ke yin a ganin sun hana wa yan siyasa siyan kuri’u a babban zaben kasar da za a fara gudanarwa a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana cewa za ta biya lada ga duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’u a zaben.

Mai Magana da yawun hukumar ta EFCC, Tony Orilade ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Laraba 13 ga watan Fabrairu a Abuja. Ya ce wannan tsari na daga cikin tsarin busa usur din fallasa masu harkallar kudade da EFCC ta shigo da shi.

Duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’a za mu biya shi lada – EFCC

Duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’a za mu biya shi lada – EFCC
Source: Getty Images

Orilade ya ce Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya gargadi duk mai saye da mai saidawa cewa su kuka da kan su, domin idan an kama su, za su fuskanci hukunci.

Magu ya ce a cikin dokar zabe ta 2010, akwai sashe na 124 wanda ya ce hukuncin tara ta naira 500,000 ta hau kan wanda aka kama ya na sayen kuri’u da shi ma mai sayarwar.

KU KARANTA KUMA: Zamfara: APC ta mika sunayen ‘yan takara ga INEC

Ya ce akwai karin dauri na watanni 12 ko mutum ya biya tara, ko kuma a hada masa biyun duka.

Magu ya ce sun samu bayanin cewa akwai wasu ‘yan siyasa da su ka yi kokarin shigo da kudade daga waje domin su rika sayen kuri’u. Ya ce sun toshe hanyar da za su iya shigo da kudaden.

Daga nan sai ya yi kiran cewa kada a yi nauyin kafa, da an ga masu dillancin sayen kuri’u, to a gaggauta sanar da EFCC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel