Harin Boko Haram: Hadiman Gwamna Shettima sun ga baiken sa a kan kin amfani da motoci ma su garkuwa

Harin Boko Haram: Hadiman Gwamna Shettima sun ga baiken sa a kan kin amfani da motoci ma su garkuwa

- Wata majiya ta bayyana cewa masu tsaron Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno basu jin dadin yada ya ke kin amfani da mota mai garkuwa

- Gwamna Shettima ya na kin amfani da motocci masu garkuwa ne saboda yana ganin yin hakan ba adalci bane ga masu tsaronsa da sauran 'yan tawagarsa

- Majiyar ta ce gwamnan jarumi ne amma ta mahangar tsaro rashin amfani da mota mai garkuwa kuskure ne musamman ga gwamna da ke jihar da ke fama da kallubalen tsaro kamar Borno

Bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai ga tawagar Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Talata 12 ga watan Fabrairu, wata majiya daga hukumomin tsaro ta bayyanawa Premium Times cewa masu tsaron gwamnan sun dade suna fama da shi a kan rashin kin amincewa ya yi amfani da mota mai garkuwa.

A kalla mutane biyar ne aka kashe a ranar Talata ciki har da soja guda daya a yayin da mayakan Boko Haram suka kai hari ga tawagar na Gwamna Shettima a hanyarsu ta Maiduguri zuwa Gamboru.

DUBA WANNAN: Kungiyar Tijjaniya tayi karin haske a kan goyon bayan takarar Buhari

Harin Boko Haram: Hadiman Gwamna Shettima sun ga baiken sa a kan kin amfani da motoci ma su garkuwa

Harin Boko Haram: Hadiman Gwamna Shettima sun ga baiken sa a kan kin amfani da motoci ma su garkuwa
Source: Depositphotos

Majiyar da ya nemi a boye sunansa ya ce rashin amincewa da amfani da motocci masu garkuwa da gwamnan keyi ya dade yana damun masu tsaronsa. Ya ce gwamnan baya son amfani da motoci masu garkuwar duk da cewa yana da guda biyu a gidan gwamnati.

A cewarsa, ana amfani da su ne kawai idan za a dako muhimman baki da suka kawo wa gwamnan ziyara a jihar Borno.

Majiyar ya ce, gwamnan yana ganin ba dai-dai bane a matayinsa na shugaba shi kadai ya shiga mota mai garkuwa yayin da sauran masu tsaronsa za su shiga mota mara garkuwar.

"Yana ganin tafiya cikin mota mai garkuwa zai iya jefa tsoro a cikin zukatan masu tsaronsa da sauran hadimansa," inji shi.

Ya ce idan aka duba lamarin da mahangar tsaro, gwamnan ya yi kuskure saboda a matsayinsa na gwamnan jihar, shine wanda 'yan ta'adda da sauran miyagu za su nemi su kashe ko ta wane hali ne.

"Babu shakka gwamnan jarumi ne kuma yana da hujja a amma a mahangar tsaro abinda ya keyi ba dai-dai bane. Masu tsaronsa sun dade suna fama da shi saboda kin amfani da mota mai garkuwa kuma duk da hakan baya tsoron zuwa wuraren da ke da hadari."

Da aka nemi ji ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya ce ba zai iya tsokaci a kan lamarin ba saboda batu ne da ya shafi harkar tsaro. Ya ce gwamna ne kadai ko kuma babban dogarinsa zai iya sharhi a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel