Dubban mutane sun yi tururuwan fitowa domin tarban Buhari a Katsina

Dubban mutane sun yi tururuwan fitowa domin tarban Buhari a Katsina

Dubban mogoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress sun yi tururuwa a jihar Katsina, inda suke jira isowar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da gangamin kamfen dinsa a mahaifar tasa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa wasu magoya bayan da suka isa birnin tun a ranar Laraba sun kwana a wajen unguwanni duk da tsananin sanyin da ake yi.

NAN ta kuma ruwaito cewa tuni filin wasa na Muhammad Dikko inda za a gudanar da gangamin ya cika ya tunbatsa.

Dubban mutane sun yi tururuwan fitowa domin tarban Buhari a Katsina

Dubban mutane sun yi tururuwan fitowa domin tarban Buhari a Katsina
Source: UGC

Tuni masu motoci suka ajiye motocinsu a gefe don yin tafiyar kilomita goma zuwa filin kamfen din saboda yawan cunkoson jama'a da ababen hawa.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: PDP ta koka kan yawan matakan tsaron da aka tura Kwara

Ana sanya ran Buhari sai kammala kamfen dinsa a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu a Katsina sannan daga nan zai garzaya Daura inda anan ne zai kada kuri'arsa na zaben shugaban kasa a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu wanda shima ya kasance daya daga cikin masu takara.

An kuma tattaro cewa akwai cunkoson ababen hawa a hanyoyin da ke sada mutun da babbar birnin jiar ta Jibia, Batsari, Kaita, Daura, Mani, Dutsinma da Kankia yayinda magoya bayan APC a fadin kananan hukumomi 31 na jiarr ke tururuwan zuwa taron.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel