Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

Jami'an 'yan sanda a Kano sun kama buhuna 14 da aka cika makil da kuri'un zabe da ake dangwale a unguwar Sabon Gari da ke jihar ta Kano.

Kwakwaran majiya ta tabbatar wa Daily Nigerian cewa an riga an dagwale kuri'un zaben inda aka dangwala wa jam'iyyar All Progressives Congress.APC.

A halin yanzu dai an tafi da buhuhunan takardun zaben zuwa hedkwatan 'yan sanda domin a cigaba da bincike.

DUBA WANNAN: Kungiyar Tijjaniya tayi karin haske a kan goyon bayan takarar Buhari

Kano: An kama buhu 17 makare da kuri'u da aka dangwale

Kano: An kama buhu 17 makare da kuri'u da aka dangwale
Source: UGC

Sai dai a cikin wata sanarwar gaggawa da ya fitar, Kakakin 'yan sanda na jihar Kano, Haruna Abdullahi ya ce kuri'un zaben da aka kama ba na ainihi bane, an wallafa su na a matsayin gwaji kuma ba a dangwale su ba kamar yadda rahotanin baya suka bayyana.

Mr Abdullahi ya ce wadanda aka kama da takardun sun ce suna hanyarsu ne zuwa jihar Jigawa inda za ayi amfani da kuri'un zaben domin wayar da kan mutane yadda za su kada kuri'a a ranar zabe.

"Kuri'un zaben da aka kama ba a dangwale su ba kuma ba kuri'u na ainihi bane. Kuri'u ne kawai na gwaji da za ayi amfani da su wurin wayar da kan masu zabe a jihar Jigawa," inji shi.

Mr Abdullahi ya kara da cewa wadanda aka kama da kuri'un zaben sun tabbatar masa cewa suna hanyarsu ta zuwa jihar Jigawa ne inda za ayi amfani da kuri'un wurin wayar da kan masu jefa kuri'a a karkara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel