Buhari zai samu kuri’u miliyan 10 daga matasa – Kungiyar kamfen

Buhari zai samu kuri’u miliyan 10 daga matasa – Kungiyar kamfen

- Daraktan kungiyar matasa a kamfen din Buhari, Wole Aboderin ya sha alwashin cewa zai samarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’u miliyan 10 a yakinsa na neman tazarce

- Aboderin yace sun isar da sakonni ga al’umman karkara akan nasarorin shugaban kasa a shekaru uku da suka gabata don masu kada kuri’u su cigaba da marawa cigaba baya

- Yace matasa maza da mata sun amfana daga shiriye-shiryen shugaban kasar na tallafawa marasa aikin yi

Daraktan harkokin mata da matasan kungiyan yakin neman zabe na Buhari/Osinbajo, Wole Aboderin, a jiya ya sha alwashin cewa zai samarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’u miliyan 10 a yakinsa na neman tazarce.

Aboderin ya bayyana cewa kungiyar yakin neman zaben wacce uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ke jagoranta, ta isar da sakonni ga al’umman karkara akan nasarorin shugaban kasa a shekaru uku da suka gabata don masu kada kuri’u su cigaba da marawa cigaba baya.

Buhari zai samu kuri’u miliyan 10 daga matasa – Kungiyar kamfen

Buhari zai samu kuri’u miliyan 10 daga matasa – Kungiyar kamfen
Source: Depositphotos

Yace matasa maza da mata sun amfana daga shiriye-shiryen shugaban kasa Buhari na Social Investment Project wanda ya samarwa matasa da dama aikin yi.

“Matasa sun fahimci cewa Buhari yana shinfida matakalan cigaban kasar Najeriya ne kuma dole a tallafawa wannan aikin har na tsawon shekaru hudu masu zuwa,” a cewar shi.

KU KARANTA KUMA: Ba za ku yi danasanin sake bani kuri’unku ba - Buhari

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa hugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a yau misalin karfe 7 na yamma kuma za a maimaita jawabin a gidajen rediyo da talabijin da karfe 9 na daren yau.

Sanarwar ta kara da cewa "Ana umurtar dukkan tashohin rediyo da talabijin da sauran kafafen yada labarai su karkata zuwa ga tashohin talabijin na kasa wato Nigerian Television Authority NTA domin watsa jawabin na shugaban kasa."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel