Amurka, Turai na adawa da shugaban kasa Buhari - Abba Kyari

Amurka, Turai na adawa da shugaban kasa Buhari - Abba Kyari

- Shugaban Ma'aikatan Buhari, Abba Kyari, ya yiwa Amurka da Turai wankin babban Bargo

- Abba Kyari ya ce kasar Amurka da sauran kasashen nahiyyar Turai na adawa da takarar Buhari

- Na hannun daman Buhari ya fusata kan yanayi na ruwa da tsakin manyan kasashen duniya kan zaben 2019

Mun samu cewa, Abba Kyari, shugaban ma'aikata na shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana fushin sa kwarai da aniyya dangane da salo da kuma yanayi na ruwa da tsakin manyan kasashen duniya kan babban zabe na 2019.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mallam Kyari ya yi wankin babban bargo kan manyan kasashen duniya musamman Amurka da sauran kasashe na nahiyyar Turai, dangane da rawar da suke takawa kan babban zaben kasar nan da zai gudana a ranar Asabar ta jibi.

Abba Kyari tare da shugaba Buhari

Abba Kyari tare da shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Cikin wata wallafa da shafin jaridar ThisDay ya ruwaito, babban jami'in gwamnatin ya kausasa harshe da cewar manyan kasashen duniya na ci gaba da ikirarin soyuwar su akan tsaftataccen zabe na gaskiya da adalci da hakan ya sha bamban da manufofi na wakilai da jakadun su da ke kasar nan.

Mallam Kyari ya yi zargin cewa, manyan kasashen duniya na adawa da shugaba Buhari sakamakon tsare-tsare da akidun sa na janye dogaron kasar nan daga shigo da kayayyaki da kasashe ketare domin habakar tattalin arzikin ta.

KARANTA KUMA: Buhari da Atiku za su gudanar da taron yakin zabe na karshe a yau Alhamis

Kazalika na hannun daman shugaba Buhari ya soki tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da cewar gwamnatin baya ke da alhakin jefa kasar nan cikin duk wani kangi na tagayyara da rashin ci gaba da ake fuskanta a halin yanzu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel