Ya kamata Buhari ya bari a yiwa Amaechi gwaji na ta taɓuwar hankali - Wike

Ya kamata Buhari ya bari a yiwa Amaechi gwaji na ta taɓuwar hankali - Wike

- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nemi shugaban kasa Buhari da ya bayar da sahalewar sa wajen yiwa Ministan sa Amaechi gwaji na taɓin hankali

- Gwamna Wike ya ce ya kamata a duba lafiyar kwakwalwar Amaechi sakamakon dakikanci da ta sanya ya ke ikirarin cewar ya kulla yarjejeniyar goyon bayan shugaba Buhari a madadin samu nasarar tazarce a bisa kujerar sa ta gwamna

- Nyesom ya ce Buhari ya kunyata shi sakamakon yadda ya zuba idanu kurum yayin da Amaechi ke ci gaba da yiwa al'ummar jihar Ribas barazanar ta'addanci

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnan jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, na neman lamuni da yarjewar sa akan yiwa Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, gwaji na taɓin hankali.

Yayin yakin zaben sa da ya gudanar cikin birnin Fatakwal, Wike cikin jawaban sa ga magoya baya ya yi kira na neman sahalewar shugaban Najeriya wajen yiwa Minista Amaechi gwaji na tabbatar da cikakkiyar lafiyar kwakwalwar sa.

Gwamnan jihar Ribas; Nyesom Wike

Gwamnan jihar Ribas; Nyesom Wike
Source: Depositphotos

Gwamna Wike ya jinginawa Amaechi ciwo na taɓuwar hankali sakamakon ikirarin da ya yi a kansa na cewar ya na goyon bayan shugaba Buhari domin wurin shiga da zai yi tasiri wajen tabbatar da nasarar sa akan kudirin tazarce da ya sanya gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa, jagoran al'ummar jihar Ribas ya musanta ikirarin Amaechi da ya shelanta kan cewa shi Gwamna Wike a karan kansa na bege gami da rokon shugaban kasa Buhari da ya zame masa madogara ta komawa bisa kujerar sa ta Gwamna a karo na biyu.

Kazalika Wike ya bayyana takaicin sa na jin kunya dangane da yadda shugaba Buhari ya zuba idanu kan Amaechi ba tare da wani mataki ba yayin da ya yiwa al'ummar jihar Ribas barazanar ta'addanci.

KARANTA KUMA: Amurka, Turai na adawa da shugaban kasa Buhari - Abba Kyari

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Amaechi wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Ribas ya sha alwashi na sai inda karfin sa ya kare wajen hana gwamna Wike komawa bisa kujerar sa, sakamakon rashin ladabi da bai samu tamkar Karen Farauta da uban gidansa.

Da yake gabatar jawabai yayin taron yakin neman zaben Buhari da aka gudanar cikin jihar Ribas a ranar Talatar da ta gabata, Amaechi ya bugi kirji da cewar ya na da tasiri mai girman gaske akan duk wata nasaba ta siyasa da Wike ya samu a rayuwar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel