Yadda Boko Haram suka kai mana hari a jiya - Gwamna Shettima

Yadda Boko Haram suka kai mana hari a jiya - Gwamna Shettima

- Gwamnan jihar Borno ya jajantawa iyalan mutane 3 da suka rasa rayukan su a kamfen din shi a Gamboru sakamakon hari Boko Haram

- Ya bawa jami'an tsaro umarnin kawo cikakke kuma gamsasshen bayani akan faruwar hakan

- Hakan ba zai sa ya ga gazawar sojin Najeriya ba na sadaukarwar su

Yadda Boko Haram suka kai mana hari - Gwamna Shettima

Yadda Boko Haram suka kai mana hari - Gwamna Shettima
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bada bayani akan yanda wadanda ake zargin yan ta'addan Boko Haram ne suka kai hari ga tawagar kamfen din shi a ranar talata wanda hakan ya kawo ajalin mutane 3 a tawagar shi.

A wata magana ta mai bada shawar na musamman ga gwamnan akan sadarwa da tsari, Isa Gusau, gwamnan yayi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su kuma zai je ya sadu da iyalan a yau.

Kamar yanda rahoton farko ya fada, mutane uku ne suka rasa rayukan su kuma gwamnan na bukatar cikakken bayani daga jami'an tsaro akan aukuwar lamarin.

Gwamnan yace "Abinda ya faru a ranar talata yayin da gwamnan ke kan hanyar shi ta zuwa Gamboru don cigaban kamfen din shugaban kasa da yan majalisar dattawa da za a yi a ranar asabar,"

GA WANNAN: Yaki da kake da rashawa yana bisa tsari, dattijon Bayelsa ya fadi ma Buhari

"Gwamnan ya bar Maiduguri a ranar talata da safe kuma ya tsaya a Mafa da Dikwa kafin ya kama hanyar Gamboru inda ya kwana har washegari ya koma Maiduguri,"

"A ranar litinin yayi tafiya zuwa Damasak, kafin nan kuma yayi kamfen a arewacin Borno. Yayi kamfen a kananan hukumomin Chibok, Gwoza, Askira Uba da Biu."

Gwamnan yace zai je ya da kanshi don ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su, kari da cewa zai yi taro da shuwagabannin tsaro akan abinda ya farun.

Abin mara dadin ji da ya faru yace ba zai sa ya samu tantama akan karfin aikin sojin Najeriya ba wadanda suke sadaukar da farincikin su, rayukan su da yancin su don yakar Boko Haram.

Gwamnan yayi kira ga yan jihar dasu kwantar da hankalinsu tare da addu'a da kuma goyon bayan sojin da masu taimakon kai da kai.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel