Gani Adams na OPC a kasar Yarabawa, yace a zabi mai tsoron Allah a zabukan 2019

Gani Adams na OPC a kasar Yarabawa, yace a zabi mai tsoron Allah a zabukan 2019

- Basaraken kasar yarbawa Gani Adams ya hori yan Najeriya dasu zabi shuwagabanni masu tsoron Allah da suka cancanta

- Wajibin yan Najeriya ne su saka Najeriya farko kafin burin su ko ra'ayoyin su

- Yayi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da kada ta ba yan Najeriya kunya

Gani Adams na OPC a kasar Yarabawa, yace a zabi mai tsoron Allah a zabukan 2019

Gani Adams na OPC a kasar Yarabawa, yace a zabi mai tsoron Allah a zabukan 2019
Source: UGC

Aare Onakakanfo na kasar yarbawa, Gani Adams, a ranar laraba ya hori yan Najeriya dasu yi amfani da zabe mai zuwa wajen zaben Shuwagannin da suka dace kuma masu tsoron Allah a kasar nan.

Adams ya hori yan siyasa masu takara a zabukan dake gabatowa cewa su fito sak a farar hula ganin cewa yan Najeriya a shirye suke wajen ganin anyi zabe a cikin zaman lafiya.

Ya tabbatar da cewa gyara Najeriya shine matakin da Najeriya take bukata a matsayin ta na kasa.

"Muna cikin mako mai muhimmanci. Zabe zai zo ya wuce amma kuma Najeriya na nan har nan gaba,"

"Daya daga cikin kurakuren da mukeyi a matsayin yan Najeriya, muna dora kowanne nauyi akan wanda ya zama shugaban kasa ba tare da tunanin abinda zai faru nan gaba ba. Yakamata ace akwai kudiri don gyara Najeriya nan gaba kuma zaben ne mabudin hakan."

GA WANNAN: Duk abinda PDP ke shirya wa a Legas a shirye muke da martani - Amaechin APC

"Wajibin duk wani dan Najeriya da ya isa zabe da yasa a zuciyar shi cewa Najeriya ce a farko ba wai ra'ayin shi ba," inji Adams.

Yayi kira ga shuwagabannin siyasa da yan takara, na kowacce jam'iyya dasu saka Najeriya farko kafin kafin burin su.

"A misali, a zaben 2015, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya saka Najeriya farko kafin burin shi da bukatar shi. A lokacin yace burin shi bai kai jinin yan Najeriya ba. A matsayin shi na shugaban kasa, ya shugabanci zaben kuma ya mika mulki ga shugaban kasa na yanzu,"

Adams yayi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da kada ta ba yab Najeriya kunya, cewa da akwai bukatar a tsananta tsaro a akwatunan zabe.

"A samar da kayayyakin zabe isassu ga yan Najeriya don zabe," inji Adams

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel