Zaben 2019: PDP ta koka kan yawan matakan tsaron da aka tura Kwara

Zaben 2019: PDP ta koka kan yawan matakan tsaron da aka tura Kwara

- Jam'iyyar PDP tayi korafi akan yawan matakan tsaro da aka tura jihar Kwara wacce ta kasance jihar shugaban majalisan dattawa kuma babban daraktan kamfen din Atiku, Dr. Bukola Saraki

- PDP ta bayyana akan a matsayin wani makirci da jam'iyyar APC ke shiryawa don yin magudin zabe

- Jam’iyyar har ila yau ta bayyana cewa irin wadannan shirye-shirye na APC da kuma shugaba Buhari baza suyi tasiri ba

Gabannin zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) tayi korafi akan yawan matakan tsaro da aka tura jihar Kwara wacce ta kasance jihar shugaban majalisan dattawa kuma babban daraktan kungiyan yakin neman zabe na dan takaran shugaban kasa na PDP, Dr. Bukola Saraki.

A wani jawabi daga kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, yace tura jami’an tsaron ya kasance daga cikin shirin jam’iyyar All Progressive Party (APC) da Gwamnatin Tarayya don razanawa da cin mutunci, hadi da tsorata masu zabe don su samu damar yin murdiya a zabuka a jihar.

“Daga cikin shirye-shirye, hukumar DSS ya tura babban darakan ayyukanta , Etteng Bassey tare da daraktocin jihohin Ogun da Anambra zuwa Jihar Kwara gabannin zabukan ranan Asabar yayinda aka tura daraktan hukumar na jihar Kwara zuwa Benue. Wannan ya biyo bayan daruruwan jami’an da aka turo daga Abuja zuwa jihar Kwara.”

Zaben 2019: PDP ta koka kan yawan matakan tsaron da aka tura Kwara

Zaben 2019: PDP ta koka kan yawan matakan tsaron da aka tura Kwara
Source: UGC

Jam’iyyar PDP tace turo jami’an ne dalilin da yasa jam’iyyar APC ke ikirarin cewa zata lashe zabukan kasar, duk da cewa jam’iyyar adawa tayi nuni ga cewar karuwar da ta samu daga wajen al’umma ya nuna cewa PDP ce ke da nasara.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara bata wanke yan takarar APC a Zamfara ba – Sanata Marafa

Jam’iyyar PDP har ila yau ta bayyana cewa irin wadannan shirye-shirye na APC da kuma shugaba Buhari baza suyi tasiri ba, inda ta kara da cewa a shirye yan Najeriya suke don fuskantan duk wani zalunci, tare da fitar dasu daga mulki a zabe mai zuwa.

Jam’iyyan ta bukaci dukkan mambobinta da magoya bayanta da su kasance da kudurin watsar da duk wani shiri na APC. Ta kuma bukace su da su fito kwansu da kwarkwatansu don kada kuri’arsu, da tsare kuri’arsu ta hanya madaidaiciya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel