Tsautsayi ya rutsa da Ministan Najeriya yayi hadari a kan titin Ebonyi

Tsautsayi ya rutsa da Ministan Najeriya yayi hadari a kan titin Ebonyi

Mun ji cewa akalla mutum 16 ne su ka gamu da rauni a lokacin da tawagar Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya watau Dr Ogbonnaya Onu ta burmawa wani mai babban mota a kan titi a cikin jihar Ebonyi.

Tsautsayi ya rutsa da Ministan Najeriya yayi hadari a kan titin Ebonyi

Ogbonnaya Onu yayi hadari a kan hanyar zuwa garin su
Source: Facebook

Wannan abu ya faru ne a lokacin da motocin Ministan su ka aukawa wata babbar motar mai dauke da fasinjoji a daidai lardin wani barikin sojoji da ke kan hanyar garin Abakiliki zuwa cikin Afikpo kamar yadda mu ka samu labari.

Shi kuma Ministan a lokacin yana kokarin shiga cikin Garin Abakilili ne na jihar Ebonyi tare da mutanen sa. Dr. Onu yana cikin tawagar, amma an yi dace bai samu ko kwarzane ba yayin da sauran jama’a su ka samu rauni.

KU KARANTA: Buhari da Atiku za su halarci lacca da aka shirya domin tunawa da Murtala

Mai girma Ministan dai ya tsira lafiya lau kamar yadda jaridun kasar nan su ka bayyana. Wasu daga cikin wadanda ke cikin tawagar kuma sun karya kafafu da hannuwa, yayin da wasun su kuma su ka samu rauni iri-iri a kan su.

Mutane kimanin 16 da ke cikin motocin Ministan su na babban asibitin koyon aiki na jami’ar Ebonyi da ke Abakaliki yanzu haka inda ake kokarin ceto ran su. Wasu da ke cikin motar ma dai su na cikin wani mawuyanci hali yanzu.

Wani Bawan Allah mai suna Lawrence Onojo yana cikin wadanda su ka jikkata a hadarin inda ya fasa kai ya kuma samu karaya. Onojo yake cewa motar Ministan ta wuntsula ta koma wani hannu inda su kayi karo da wasu motoci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel