Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun bankawa ofishin yan sanda wuta (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun bankawa ofishin yan sanda wuta (Hotuna)

Wasu matasa maras jin magana sun bankawa ofishin jami'an hukumar yan sanda dake Ajali, karamar hukumar Orumba wuta a jihar Anambara, kudu maso gabashin Najeriya.

Kafin kona ofishin, yan barandan sun saki dukkan wadanda ke tsare a kurkukun yan sandan, rahotanni sun bayyana.

Hotuna daga wajen gobaran yan nuna cewa an kona ofishin yan sandan kurmus da wasu motocin yawon yan sanda guda biyu. Amma kakakin yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya ce ba haka bane. Innama gobara ne kawai.

Yace: "Zamu dauki wannan hadari matsayin gobara har sai bincike ya bayyana ba hakan bane. Kwakishanan yan sandan jihar na wajen yanzu domin ganin abinda ya auku."

"Ya umurci sashen bincike da leken asiri da su gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abinda ya faru."

Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun bankawa ofishin yan sanda wuta (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun bankawa ofishin yan sanda wuta (Hotuna)
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun bankawa ofishin yan sanda wuta (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun bankawa ofishin yan sanda wuta (Hotuna)
Source: UGC

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel