Ba za ku yi danasanin sake bani kuri’unku ba - Buhari

Ba za ku yi danasanin sake bani kuri’unku ba - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa yan Najeriya tabbacin cewa baza suyi danasani ba idan har suka sake zabarsa

- Buhari yace gwamnatinsa tayi tsayin daka wajen ganin ta cika alkawaran da ta dauka na yakin neman zabe wadanda suka hada da bunkasa tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da rashawa

- Shugaban kasar ya kara jadadda cewa zai bincikikudi kimanin dala biliyan 16 da gwamnatin PDP ta kashe a wutan lantarki ba tare da ganin sakamako ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa yan Najeriya tabbacin cewa baza suyi danasani ba idan har suka sake bashi damar zama shugaban kasarsu a karo na biyu.

Buhari ya ba da tabbacin ne a yayinda yake gabatar da jawabi a taron yakin neman zaben jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na kasa dake a babban birnin Tarayya, Abuja.

Shugaban kasar yace gwamnatinsa tayi tsayin daka wajen ganin ta cika alkawaran da ta dauka na yakin neman zabe wadanda suka hada da bunkasa tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da rashawa.

Ba za ku yi danasanin sake bani kuri’unku ba - Buhari

Ba za ku yi danasanin sake bani kuri’unku ba - Buhari
Source: UGC

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa al’umman birnin tarayya da al’umman arewa maso gabas sun kasance shaida akan inganci da aka samu akan lamarin tsaro, ya bayyana cewa hukumomin tsaro a halin yanzu suna iya kokarinsu don ganin sun magance rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Benue da kuma rigingimu da wasu yan fashi ke haddasawa a jihar Zamfara.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara bata wanke yan takarar APC a Zamfara ba – Sanata Marafa

Ya bayyana cewa tare da samar da taki ga manoma a farashi mai rahusa, Najeriya ta daina shigo da shinkafa fiye da kashi 90 cikin dari. Yace kudade da aka samu ta fannin noma ne aka yi amfani dasu wajen samar da tituna, hanyoyin jirgin kasa da kuma wutar lantarki.

Akan yaki da rashawa, shugaban kasar ya kara jadadda cewa zai bincikikudi kimanin dala biliyan 16 da gwamnatin PDP ta kashe a wutan lantarki ba tare da ganin sakamako ba a wutan lantarki.Ya roki kasashen ketare dasu taimaki Najeriya wajen dawo da kudadenta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel