Kotun daukaka kara bata wanke yan takarar APC a Zamfara ba – Sanata Marafa

Kotun daukaka kara bata wanke yan takarar APC a Zamfara ba – Sanata Marafa

Shugaban kwamitin man fetur a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Garba Marafa ya bayyana cewa hukunce-hukunce daga kotunan roko biyu na Abuja da Sokoto shine cewa APC bata da dan takara a Zamafara yanzu.

“Mun koma shafin farko, wato kenan babu dan takara na APC a Zamfara, inji shi.

Jawabin Marafa yace: “ Sabanin bayanai da wasu mutane ke yayatawa, kotun roko da ke Sokoto bata wanke yan takarar APC a Zamfara ba.

Kotun daukaka kara bata wanke yan takarar APC a Zamfara ba – Sanata Marafa

Kotun daukaka kara bata wanke yan takarar APC a Zamfara ba – Sanata Marafa
Source: Depositphotos

“A bangaren Sokoto, kotun roko taki ta amince da korafin da lauyan Yari yayi na neman a tursasa amfani da hukuncin babbar kotun Zamfara. Am dage tursasa hukuncin ne bisa ga rokon da dan majalisar wakilai Sani Jaji yayi sannan aka janye lamarin don haka aka yi watsi da shi.

“A bangaren Abuja, kamar waccan lauyan Yari da kansa ya janye karar da ya shigar domin cewa ba wai Justis Ijeoma Ojukwu ta bayar da wani umurni bane kawai dai ta yaba ma INEC ne inda tace hukumar ta yanke hukunci ne a karfin ikonta sannan cewa APC ya gaza tabbatar da kararta na cewa ta gudanar da zaben fidda gwani a Zamfara.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Yan sanda sun gargadi yan siyasa akan siyan kuri’u

"Don haka sai ta yi watsi da karan.Saboda haka karara ya nuna cewa mun koma baya APC bata da yan takara a Zamfara.

"Bayanai da ake yadawa a shafukan zumunta ba komai bane face karya da tuggun wasu yan siyasar dake tsoron komawa gida na dole, don haka a watsar da zancensu."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel