Daruruwan mambobin APGA sun sauya sheka zuwa PDP a Anambra

Daruruwan mambobin APGA sun sauya sheka zuwa PDP a Anambra

- Daruruwan magoya bayan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar Anambra sun sauya sheka zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP)

- Hakan na zuwa ne kwanaki biyu kacal kafin zaben shugaban kasa da na yan majalisar dokokin kasa

- Masu sauya shekar sun hada da tsoffin shugabannin APGA da kuma jami’an jam’iyyar

Yayinda ake shirin fara zaben kasa a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, daruruwan magoya bayan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar Anambra sun sauya sheka zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Majiyarmu ta ruwaito cewa masu sauya shekar sun fito daga kananan hukumomi 21 na jihar sannan sun hada da tsoffin shugabannin APGA da kuma jami’an jam’iyyar.

Da yake jawabi a taron yi masu maraba, daraktan kamefen din takarar shugaban kasa na PDP a jihar Anambra, Dr. Harry Oranezi ya bayyana hukuncin masu sauya shekar a matsayin wanda ya dace inda yace wadanda ke adawa dasu na akan hanya mara billewa.

Daruruwan mambobin APGA sun sauya sheka zuwa PDP a Anambra

Daruruwan mambobin APGA sun sauya sheka zuwa PDP a Anambra
Source: Depositphotos

Daraktan kamfen din ya bukaci sabbin mambobin jam’iyyar da su yi gaggawan shiga daga cikin harkokin jam’iyyar domin a dama dasu, cewa PDP ce kadan za ta iya fitar da kasar daga halin da take ciki a yanzu.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Yan sanda sun gargadi yan siyasa akan siyan kuri’u

Ya bukace su da su tabbatar da cewar dukkanin yan takarar jam’iyyar sun yi nasara a matakin jiha da zaben shugaban kasa yayinda ya basu tabbacin cewa jam’iyyar zata saka masu bisa goyon bayan da suka bata.

Da yake yaba ma matakin a suka dauka na dawo wa jam’iyyar, Oranezi ya shawarce su da suyi amfani da manuniyarsu wajen kada kuri’a maimakon babban yatsa don ganin sun fatattaki duk wani dan takara da ba dan PDP bane.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel