Mu-hadu-a-2023: Buhari ne zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye - Hon Abdulmumini Jibrin

Mu-hadu-a-2023: Buhari ne zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye - Hon Abdulmumini Jibrin

Ku tari 2023, don 2019 ta Buhari ce - Sakon Abdulmumin Jibrin ga 'yan PDP

Dan majalisar tarayyar nan mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Bebeji da Kiru daga Kano da yanzu haka yake a matsayin korarre daga majalisar Alhaji Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa yanzu kam ta tabbata shugaba Buhari zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye.

Dan majalisar da ya bayyana hakan a shafin sa na sada zumuntar Tuwita ya kuma bayyana nasarorin da shugaban kasar ya samu tare kuma da jam'iyyar adawa marar karfi a matsayin wasu dalilan da za su sa shugaban ya sake lashe zaben cikin ruwan sanyi.

Mu-hadu-a-2023: Buhari ne zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye - Hon Abdulmumini Jibrin

Mu-hadu-a-2023: Buhari ne zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye - Hon Abdulmumini Jibrin
Source: Depositphotos

KU KARANTA: 'Yan sanda sun zagaye ofishin INEC a Fatakwal

Legit.ng dai ta samu cewa daga nan ne ma dai sai dan majalisar ya shawarci dukkan 'yan Najeriya musamman ma dai yan siyasa dake tunanin yin takara da shugaba Buhari din da su hutar da kan su su fara tanadin 2023.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar mai mulki a tarayyar Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta bayyana takaicinta kan yadda aka jefi shugabanninta da suka hada da shugaba Muhammadu Buhari a gangamin yakin neman zaben shugaba Buhari a jihar Ogun.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jam'iyyar ta APC ta fitar inda ta ce za ta dauki tsattsauran mataki kan gwamnan jihar Ibikunle Amosun wanda ta zarga da shirya cin mutuncin ga Buhari da kuma shugabanta Adams Oshiomhole.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel