Zaben 2019: Shugaba Buhari ya kara samun goyon baya daga yankin su Jonathan

Zaben 2019: Shugaba Buhari ya kara samun goyon baya daga yankin su Jonathan

Wata kungiya ta tsaffin tsagerun 'yan yankin Neja Delta dake da arzikin man fetur ta Peace Ambassadors of Niger Delta (PAND) a turance ta sanar da goyon bayan ta ga takarar tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben da za'a gudanar a karshen satin nan.

Wannan dai kamar yadda muka samu yana kunshe ne a cikin wata sanarwar matsaya ta bayan taro dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta Peace Ambassadors of Niger Delta (PAND) Mista Ebikabowei Victor bayan karshen taron su na yini daya a garin Fatakwal.

Zaben 2019: Shugaba Buhari ya kara samun goyon baya daga yankin su Jonathan

Zaben 2019: Shugaba Buhari ya kara samun goyon baya daga yankin su Jonathan
Source: UGC

KU KARANTA: Gwamnati ta gano hanyar da PDP ta shirya gurgunta zaben 2019

Legit.ng Hausa ta samu daga majiyar ta kamfanin dillacin labaru cewa kungiyar ta Peace Ambassadors of Niger Delta (PAND) ta shirya wani taro ne na wuni daya don ganin an aiwatar da zabukan na shekarar 2019 cikin lumana.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa tsohon shugaban kasar Najeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya fito ne daga jihar Bayelsa dake zaman daya daga cikin jahohin yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Maryam Gidado wadda aka fi sani da Maryam Babban Yaro ta bi bayan jarumi Adam A. Zango inda ta bayyana goyon bayan ta ga jarumin game da sauya shekar da yayi a siyasance.

A cewar ta, ko kusa bai kamata mutane su ga laifin jarumin ba domin kuwa kowa yanayin siyasa ne domin ya samu wani abu kuma ya samu kima da daraja musamman ma a wurin mutanen da ake yi domin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel