2019: Masu gudun hijira a jahar Zamfara ba zasu yi zabe ba – hukumar INEC

2019: Masu gudun hijira a jahar Zamfara ba zasu yi zabe ba – hukumar INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta haramta ma yan gudun hijira a jahar Zamfara kada kuri’a a yayin zaben 2019, don haka ba zata shirya zabe a sansanonin yan gudun hijiran jahar ba, saboda a cewarta bata da cikakken bayanansu.

Kwamishiniya INEC mai kula da jahar Zamfara, Asmau Maikudi ce ta sanar da haka a yayin da take zantawa da manema labaru a ranar Laraba, 13 ga watan Feburairu a garin Gusau na jahar Zamfara, inji rahoton Legit.ng.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta nemi INEC ta fasa gudanar da zabe a jahar Zamfara

“Bamu da wani tsarin gudanar da zabe a sansanin yan gudun hijira a yayin babban zaben 2019 sakamakon bamu da bayanai game da sansanonin, sai dai mun hada kai da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a dukannin yankunan jahar.

“Sanin kowa ne cewa daga cikin kananan hukumomi guda goma sha hudu, guda biyu ne kacal suke da saukin matsalar tsaro, Gumi da Bakura, amma hukumomin tsaron sun bamu tabbacin samar da tsaro a duk fadin jahar.” Inji ta.

Haka zalika kwamishina Asmau ta bayyana cewa wadanda suka yi gudun hijira daga yankunansu zuwa wasu yankuna na daban zasu iya samun damar yin zabe a zaben shugaban kasa, saboda na’urar tantance kati za ta gano rumfar zabensu.

“Amma a duk inda aka samu mummunan matsalar tsaro, za’a dauke masu zaben zuwa yankin da babu matsalar mafi kusa domin baiwa jama’a hakkinsu na yin zabe. Mun yi ma nakasassu 2,020 rajist tare da basu katin zabensu.

“Haka nan mun yi sabbin masu zabe 1,717,128 rajista a zagayen sabon rajistan daya gabata, kuma akwai katin zabe fiye da 50,000 da ba’a amsa ba, wanda zamu bada ajiyansu a babban bankin Najeriya, CBN har sai bayan zaben 2019.” Inji ta.

Daga karshe Asmau ta jaddada manufar INEC na shirya zabe mai tsafta, sahihi kuma ingantacce, don haka ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki dasu bata goyon baya domin samun nasarar zaben gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel