Umarnin kama tsohon Alkalin Alkalai: Onnoghen ya ruga gaban kotu neman mafaka

Umarnin kama tsohon Alkalin Alkalai: Onnoghen ya ruga gaban kotu neman mafaka

Korarren Alkalin Alkalan Najeriya, mai sharia Walter Onnoghen ya ruga gaban kotun daukaka kara a guje a ranar Laraba, 13 ga watan Feburairu inda ya nemi kotun ta dakatar da umarnin da kotun da’ar ma’aikata, CCB, ta bayar da a kamo mata shi.

Legit.ng ta ruwaito kimanin kwanaki biyu da suka gabata ne kotun da’ar ma’aikata ta umarci Yansanda da jami’an hukumar DSS dasu kamo mata Onnghen sakamakon kin amincewa ya halarci zaman sauraron karar da aka shigar da shi gabanta, game da tuhumar kin bayyana kadarorinsa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta nemi INEC ta fasa gudanar da zabe a jahar Zamfara

Sai dai Onnghen ya shaida ma kotun daukaka kara dalilinsa na kin halartar zaman sauraron karar da aka shigar da shi, inda yace dalilin shine kotun CCB bata nemi ganinsa a yayin zaman sauraron karar ba.

Ya kara da cewa tun farko ma bai kamata kotun ta nemi a kamashi ba saboda ya shigar da kara a gaban wata kotu ta daban inda yake kalubalantar hurumin kotun CCB na sauraron karar da aka shigar da shi gabanta, kuma ba’a yanke hukunci ba har yanzu.

“Don haka ina ganin har sai an kammala shari’ar da na shigar na kalubalantar hurumin kotun CCB, kuma an yanke hukunci, babu bukatar na gurfana gaban kotun CCB, kuma ba dole bane, don haka umarnin da ta bayar na a kamani ya keta hakkina kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta bani.” Inji shi.

Haka zalika tsohon Alkalin Alkalan ya nemi shugaban kotun da’ar ma’aikata, CCB, Mai Sharia Danladi daya janye kansa daga sauraron karar da aka shigar da shi gaban kotun, saboda shima akwai zargin cin hanci da rashawa akansa.

“Ina kira ga kotu da ta bada umarnin kafa sabuwar kwamiti a kotun da’ar ma’aikata da za ta saurari karar da aka shigar da ni, sa’annan kotu ta yi kawar da umarnin da kotun CCB ta bayar na lallai sai na gurfana gabanta.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel