Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta nemi INEC ta fasa gudanar da zabe a jahar Zamfara

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta nemi INEC ta fasa gudanar da zabe a jahar Zamfara

A yayin da zabe ya rage saura kwanaki biyu kacal, wata sabuwata fito daga fadar shugaban kasar Najeriya, inda ministan shari’a kuma babban lauyan kasar, Abubakar Malami ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da kada ta gudanar da zabe a jahar Zamfara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malami ya bayyana haka ne cikin wata wasika mai dauke da shafuka uku daya aika ma hukumar INEC, inda ya nemi ta dage gudanar da zaben gwamna, yan majalisun jaha da na tarayya har sai APC ta samu halastattun yan takararu a mukaman gaba daya.

KU KARANTA: Siyasar Kano: Bana shakkar Kwankwaso a takarar da muke yi –Shekarau

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta nemi INEC ta fasa gudanar da zabe a jahar Zamfara

Shugaban INEC da Malami
Source: UGC

Idan za’a tuna an samu hatsaniya a jam’iyyar APC tsakanin bangaren gwamnan jahar Abdul Aziz Yari da na wasu jiga jigan yan siyasar jahar su takwas a karkashin jagorancin Sanata Kabiru Marafa, wanda hakan ya kasa barin APC samun halastattun dan takarar gwamna da sauran kujerun majalisun dokoki.

Malami ya bayyana cewa ya nemi INEC ta dage zaben ne bayan samun hukuncin kotun daukaka kara dake jahar Sakkwato, wanda ta bayyana cewa APC ta gudanar da zaben fidda gwani ingantacce, don haka tana da halastattun yan takarkaru a duka kujerun siyasa.

“Duba da huluncin da kotun daukaka kara ta yanke dake tabbatar da ingancin zaben fidda gwanayen yan takarkaru da APC ta shirya, don haka jam’iyyar APC a Zamfara na neman karin lokaci don shirya ma zaben yadda ya kamata, wannan hakki ne da take da shi ba wai alfarma za’a mata ba.

“Don haka ina kira ga INEC da ta yi biyayya ga umarnin kotun daukaka kara ta hanyar amincewa da sakamakon zaben fidda gwani da APC ta gabatar a Zamfara, tare da bin umarnin sashi na 38 na dokokin zabe daya baiwa INEC daman dage zaben gwamnoni, yan majalisun tarayy da na majalisun jihohi idan bukatar hakan ya kama.” Inji shi.

Sai dai lauyan Kabiru Marafa, Dauda Lawal da sauran yan takarar dake adawa da Gwamna Yari, Mike Ozekhome ya nemi INEC ta yi watsi da umarnin Ministan Sharia, inda ya bayyana umarnin a matsayin zagon kasa ga karar da suka shigar gaban kotun.

Malami ya shaida ma INEC cewa kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin babbar kotun jahar Zamfara da ta amince da cewa APC ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani, sa’annan ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da bayyana cewa APC bata gudanar da ingantaccen zabe ba.

Da wannan ne Malami ya jaddada ma INEC cewa kotun daukaka kara ta raba gardama, don haka akwai bukatar INEC ta dage gudanar da zaben da ta shirya har sai jam’iyyar APC ta kammala shiri, domin kuwa INEC bata da hurumin hana yan takara ko wata jam’iyya shiga takara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel