Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun sake samun gagarumar nasara a Madagali

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun sake samun gagarumar nasara a Madagali

Dakarun Sojin Najeriya na bataliya ta 143 daga runduna ta 28 sun sake samun gagarumar nasara akan mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a garin Madagali na jahar Adamawa bayan wani mummunan karanbatta da suka sha.

Shelkwatar rundunar Sojan kasa ta bayyana cewa an sha wannan dauki ba dadi tsakanin Sojoji da yan ta’addan ne a ranar Talata, 12 ga watan Feburairu da misalin karfe 6:10 na yammacin ranar a lokacin da yan ta’addan suka yi kokarin kutsa kai cikin garin Madagali.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya bayyana muhimmin hakkin dake wuyan Buhari a 2019

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun sake samun gagarumar nasara a Madagali

Yaki da ta’addanci
Source: Facebook

A cikin ayarin motocin masu dauke da bindiga guda biyar yan ta’addan suka kaddamar da hare harensu, sai dai nan take Sojojin Najeriya suka mayar musu da biki ta hanyar bude musu wuta babu kakkautawa.

Legit.ng ta ruwaito a sakamakon wannan fin karfi da dakarun Sojin Najeriya suka nuna ma Boko Haram yasa suka kashe wasu gagga gaggan yan ta’adda guda biyar, yayin da sauran suka ranta ana kare dauke da raunuka da suka samu a dalilin bude wutan.

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun sake samun gagarumar nasara a Madagali

Yaki da ta’addanci
Source: Facebook

Bugu dsa kari Sojojin sun kama wata motar yaki mai dauke da bindiga guda daya, makamin harba gurneti, gurneti guda hudu, bindiga kirar AK-47 guda goma sha hudu, bindiga kirar FN Rifle guda daya, wayar hannu kirar Techno da alburusai da dama, sa’annan sun lalata motoci guda biyu da bindigar AA.

Sai dai an samu wani jami’in Soja guda daya daya samu rauni a sakamakon karanbattan wanda a yanzu haka yana samun kulawa a asibiti, yayin da Sojan sa kai guda daya na rundunar Civilian JTF ya rasa ransa.

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun sake samun gagarumar nasara a Madagali

Yaki da ta’addanci
Source: Facebook

Daga safiyar Laraba kuma, Sojojin sun sake bankado gawarwakin wasu yan ta’adda guda shida, tare da bindigun AK 47 guda hudu, bindigar RN Rifle, da kuma bamabamai guda biyu, da wannna ne babban kwamandan yaki da yan ta’adda, Birgediya Abdul Malik Biu ya jinjina ma Sojojin.

Daga karshe kuma yayi kira a garesu dasu kasane suna cikin shiri a koyaushe tare da kara zage damtse a yakin da suke yi da yan ta’adda don ganin sun karshensu gaba daya, sa’annan yayi alkawarin bada kulawar da ta dace ga iyalan Sojojin da suka rasu, da kuma nay an Civilian JTF.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel