An sa ranar da za ayi shari’a da Gwamnan Adamawa da ke neman tazarce

An sa ranar da za ayi shari’a da Gwamnan Adamawa da ke neman tazarce

Mun samu labari cewa babban kotun tarayya da ke Abuja ta sa ranar da za ayi shari’a da gwamnan jihar Adamawa Sanata Mohammed Jibrilla Bindow wanda ake zargi da badakalar takardun shaida na ilmi.

An sa ranar da za ayi shari’a da Gwamnan Adamawa da ke neman tazarce

Wata kungiya tace Gwamnan Adamawa bai da takardun karatu
Source: Depositphotos

Alkali A. Adeniyi ya zabi 2 ga Watan Maris mai zuwa a matsayin ranar da zai saurari karar da aka kawo a kan Jibrilla Bindow. Wata kungiya ta kasar waje tace gwamnan yayi wa hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC karya.

Kungiyar ta Kingdom Human Rights Foundation International ta fadawa kotu cewa gwamnan yayi karya lokacin da ya fito takarar bana da yace yana da shaidar kammala Sakandare bayan ya samu lashe jarrabawar WAEC a 1983.

KU KARANTA: Manyan Kungiyoyin Duniya sun yi magana a kan zaben 2019

Wannan kungiya tace gwamnan da cewa karya yake yi bai halarci makarantar sakandaren gwamnati ta garin Miangu a cikin jihar Filato kamar yadda yake ikirari ba. Sannan kuma ana zargin sa da amfani da mabanbantan shekaru.

Wannan dai babban laifi ne wanda ya sabawa dokar kasa na final kwad da kuma tsarin zabe na Najeriya na 2010, idan har aka samu mutum da laifi, zai fuskanci shari’a. Ana gobe zabe ne dai kotu za ta yanke hukunci a kan batun.

Hakan na zuwa ne bayan mun samu labari a makon nan cewa wasu ‘yan takara fiye da 10 sun janye takarar su domin marawa gwamna mai ci Mohammed Jibrila Bindow baya a zaben da za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel