Sarki Kano da Manyan Afrika za su yi jawabi wajen taron tunawa da Murtala

Sarki Kano da Manyan Afrika za su yi jawabi wajen taron tunawa da Murtala

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku za su hadu an jima a Abuja

- A yau ne za ayi wata lacca domin tunawa da Marigayi Murtala Muhammed

- Ana sa rai kuma wasu manya da ake ji da su a Afrika su halarci wannan taron

Sarki Kano da Manyan Afrika za su yi jawabi wajen taron tunawa da Murtala

An shirya wata babbar lacca domin a tuna da Janar Murtala Mohammed
Source: Depositphotos

Mu na da labari cewa an jima ne aka tunanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar wadanda su ne manyan ‘yan takarar shugaban kasa azaben Najeriya na bana za su hadu wajen wata laccar da aka shirya yau.

A yau ne aka tsara lacca ta musamman domin tunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya Marigayi Janar Murtala Mohammed wanda aka kashe a rana irin ta jiya a shekarar 1976 lokacin yana kan karagar mulkin Najeriya a lokacin soji.

Tsohuwar shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf, da kuma Takwarorin ta na Bostawana da Tanzaniya, Festus Mogae da Jakaya Kikwete za su shigo Najeriya domin wannan taro kamar yadda mu ka samu labari a makon nan.

KU KARANTA: Kungiyar Tijjaniya ta ce ba ta goyon bayan wani 'dan takara

Shugabar gidauniyar ta Murtala Muhammed watau Aisha Muhammed-Oyebode, ta sanar da cewa Farfesa Chidi Odinkalu da kuma Madam Ayo Obe za su fara magana a wajen wannan lacca wanda aka saba yi duk shekara domin Marigayin.

Sauran wadanda za su tofa albarkacin bakin sun hada da manyan Nahiyar Afrikan irin su Dr Mohammed Ibn Chambas na majalisar dinkin Duniya da kuma Sarkin Kano Muhammad Sanusi II wanda shi ne tsohon gwamnan CBN na Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban Abokin hamayyar sa Atiku Abubakar su na cikin wadanda aka gayyata wajen taron. Ko jiya dai ‘yan takarar sun gana wajen wani taro a birnin Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel