Zabe: PDP ta bayyana matakai 4 da za ta dauka don magance magudi

Zabe: PDP ta bayyana matakai 4 da za ta dauka don magance magudi

PDP, babbar jam’iyyar adawa, ta bayyana cewar za ta yi amfani da dabaru na zamani domin tabbatar da cewar ba a yi mata magudi ba a zaben shugaban kasa da za a yi ranar asabar mai zuwa.

Shugaban tsare-tsare na kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP, Osita Chidoka, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya, Laraba, a Abuja.

Dabarun da jam’iyyar ta ce za ta yi amfani da su sun hada da kafa cibiyoyi a fadin kasar nan domin tattara sakamakon zabe, samar da lambar waya domin karbar korafi da rahoto daga ma su zabe, samar da wata kafa a dandalin sada zumunta na Tuwita domin bibiyar kada kuri’u, da kuma wata fasaha (PVT) da za ta hana ma’aikatan zabe canja sakamako ko yi wa jam’iyyar su kwange.

Za mu yi amfani da hanyoyi daban-daban domin ganin cewar ba a yi mana kwange ko magudi ba a zaben shugaban kasa.

“Za mu adana kwafin rijistar zabe da hukumar zabe ta raba ga dukkan jam’iyyu domin yin amfani da ita wajen warware matsalolin da kan iya tasowa a gaba,” a cewar Chidoka.

Zabe: PDP ta bayyana matakai 4 da za ta dauka don magance magudi

Yakin neman zaben PDP
Source: Depositphotos

Sannan ya kara da cewa jam’iyyar PDP za ta tura wakilai kwararru kuma ma su ilimi ya zuwa mazabu 176,000 da ke fadin kasar nan. Ya ce wakilan za su aiko da sakamakon zabe kai tsaye daga mazabun su ta hanyar amfani da fasahar PVT.

Chidoka ya bayyana cewar tuni jam’iyyar PDP ta kaddamar da wani layin tarho na musamman domin jama’a su kira don sanar da halin da mazabun su ke ciki ko kuma sanar da cibiyoyin jam’iyyar duk wani salo ko yunkuri na yi mata magudi.

DUBA WANNAN: Fitaccen jarumin fina-finan Hausa ya gargadi ‘yan Najeriya a kan zabe

Jam’iyyar PDP ta samar da lambobin kira da ke da turke a kan lamba kamar haka: 097000551, domin ma su zabe su kira su sanar da barkewar rikici ko kuma magudin zabe a akwatin su na zabe,” a cewar Chidoka.

Jam’iyyar PDP ta sha koka wa a kan cewar jam’iyyar APC mai mulki tare da INEC na shirin yi ma ta magudi a zabukan da za a gudanar a cikin shekarar nan. Zargin da APC da INEC su ka sha musanta wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel