Kotun daukaka kara ta fitar da sabon hukunci kan batun maganar shigar APC zabe a Zamfara

Kotun daukaka kara ta fitar da sabon hukunci kan batun maganar shigar APC zabe a Zamfara

Wata kotun daukaka kara dake zamanta a jihar Sokoto tayi watsi da daukaka karar da wani jigo a jam'iyyar APC na jihar Zamfara mai suna Aminu Jaji ya shigar a gabanta yana kalubalantar hukuncin da babbar kotun dake Gusau kan shigar jam'iyyar zaben gama gari na 2019.

Da yake bayyana rashin amincewarsa da bukatar masu karar, Lauyan Jam’iyyar APC Mahmud Magaji (SAN) ya bayyana cewar janye qarar ya sabawa dokar kotun don haka ya bukaci kotun da ka da ta aminta da janye karar.

Kotun daukaka kara ta fitar da sabon hukunci kan batun maganar shigar APC zabe a Zamfara

Kotun daukaka kara ta fitar da sabon hukunci kan batun maganar shigar APC zabe a Zamfara
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Nuhu Ribadu ya sake kwancewa PDP zane a kasuwa

A hukuncin da ta zartas Mai Shari’a Jummai Hannatu Sanki ta yi watsi da karar tare da cewar wadanda ke karar suna da dama da ‘yancin janye karar a kowane irin lokaci. A jawabin sa kan hukuncin da kotun ta yanke Lauyan APC, Magaji (SAN) ya bayyana cewar ba su da jayayya a kan matakin da kotu ta dauka.

Haka ma ya ce batun zuwa kotun koli domin qalubalantar hukuncin lamari ne da ke hannun jam’iyyar APC. Haka ma Lauyan masu kariya na 43 da 182 Mike Ozekhome (SAN) ya yabawa kotun kan watsi da karar, yana cewar yanzu ta tabbata APC ba ta da ‘yan takara a Zamfara a zaven da za a gudanar.

A zantawarsu da manema labarai Sanata Kabiru Marafa da Jaji duka sun bayyana jin daxin su ga matakin da kotun ta dauka na watsi da qarar suna cewar wannan nasara ce ga dimokuradiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel