Rashin jituwa: Shekarau ya yi karin haske a kan alakar sa da Buhari

Rashin jituwa: Shekarau ya yi karin haske a kan alakar sa da Buhari

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar sanata a jam’iyyar APC ya bude cikin sa a kan zargin rashin jituwar da ke tsakanin sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shekarau ya kasance cikin sahun gaba a sukar gwamnatin Buhari lokacin da yak e cikin jam’iyyar PDP.

Sai dai, a wata hira da ya yi da manema labarai a yau, Laraba, a gidan sa da ke Kano, Shekarau ya bayyana cewar ba a taba samun rashin jituwa tsakanin sa da shugaba Buhari.

Shekarau, tsohon ministan ilimi, ya ce tun shekarar 2002 shi da Buhari ke tafiya tare a siyasa.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa sun yi aiki tare da Buhari lokacin kirkirar jam’iyyar APC.

Rashin jituwa: Shekarau ya yi karin haske a kan alakar sa da Buhari

Shekarau
Source: Depositphotos

Ba na rigima da shugaba Buhari. Babu wani lokaci da aka taba samun rashin jituwa tsakanin mu, kuma ban taba fada wa wani cewar akwai sabani tsakanin mu ba. Na kalubalanci duk mai wata hujja a kan cewar akwai sabani tsakanina da Buhari da ya gabatar da ita.

Ni da Buhari mun dade tare. Mun yi aiki tare lokacin kirkirar jam’iyyar APC. Akwai alaka mai kyau tsakani na da Buhari,” a kalaman Shekarau.

DUBA WANNAN: Hukumar AIB ta binciko dalilin faduwar jirgin saman Osinbajo

Shekarau ya kara da cewa ko a lokacin da ya fita daga jam’iyyar APC bai yi hakan ba saboda Buhari. Sannan ya kara da cewa babu abinda ya taba alakar sa da Buhari ko yanzu da ya dawo jam’iyyar APC.

Kazalika ya yi alkawarin cewar zai yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar shugaba Buhari a zaben da za a yi a karshen mako.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel