Zabe: Rundunar ‘yan sanda ta haramtawa jami’anta rike bindiga a rumfunan zabe

Zabe: Rundunar ‘yan sanda ta haramtawa jami’anta rike bindiga a rumfunan zabe

Mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya ce sun haramta wa jami’ansu zuwa rumfar zabe dauke da bindiga, babban sufeton ya bayyana haka ne ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairu a daidai lokacin da zaben Shugaban kasa da nay an majalisar dokoki ya rage kwanaki uku kacal.

Adamu ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar tarayyar turai da ta zo sanya idanu akan zabukkan kasar ta kai masa ziyara a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Ya kuma kara jadadda musu cewa jami’ansu zasu yi aiki sanya idanu da kuma bada tsaro a rumfunan zaben.

Zabe: Rundunar ‘yan sanda ta haramtawa jami’anta rike bindiga a rumfunan zabe

Zabe: Rundunar ‘yan sanda ta haramtawa jami’anta rike bindiga a rumfunan zabe
Source: Original

Sufeton ya bayyana cewa jami’ansu zasu tabbatar da dokar nan ta takaita zirga-zirga ta yi aiki kamar yadda dokokin zabe suka tanada, sannan rundunar zata hada kai da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaro tun daga fara zaben har zuwa lokacin da za a bayyana sakamakon zaben, dama bayan zaben.

KU KARANTA KUMA: Hukumar zabe na yiwa PDP aiki - Oshiomhole

A baya legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sanda ta gargadi yan siyasa da su guji siyan kuri’u a ranar zabe ko kuma su fuskanci doka.

Mataimakin sufeto janar na yan sanda da ke kula da hedkwatar rundunar, Abuja, Usman Tilli, ya yi gargadi a Gombe a ranar Talata , 12 ga watan Janairu yayinda yake jawabi da masu ruwa da tsaki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel