Buhari zai lashe zabe ko babu kuri'un ku - Ubah ya fada wa 'yan kabilar Igbo

Buhari zai lashe zabe ko babu kuri'un ku - Ubah ya fada wa 'yan kabilar Igbo

Dan takarar Sanata na jam'iyyar APC na Anambra ta Kudu, Sanata Andy Ubah ya ce Shugaba Muhammadu Buhari zai lashe zaben ranar 16 ga watan Fabrairu ko da kuwa 'yan kabilar Ibo ba su kada masa kuri'a ba.

Ya ce zai fi dacewa 'yan kabilar Ibo zu jefawa Shugaba Muhammadu Buhari kuri'unsu saboda rashin yin hakan ba zai hana shi lashe zabe ba.

A yayin da ya ke jawabi ga magoya bayan jam'iyyan a wurin kamfen a Nnewi, Ubah ya ce al'ummar yankin ba za su maimaita kuskuren da su kayi a 2015 ba na kin zaben jam'iyyar APC a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ko da kuri'an ku ko babu Buhari zai lashe zabe - Umahi ya gargadi Ibo

Ko da kuri'an ku ko babu Buhari zai lashe zabe - Umahi ya gargadi Ibo
Source: Twitter

Ya ce 'yan kabilar Ibo su kuka da kansu idan ba su zabi Buhari da sauran 'yan takarar jam'iyyar APC a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ba.

DUBA WANNAN: Mutuwar magoya bayan jam'iyyar APC: Buhari ya mika sakon ta'aziyya

A cewarsa: "Bisa ga dukkan alamu Shugaba Muhammadu Buhari zai yi nasara a zaben ranar Asabar. Ko kun zabe shi ko ba ku zabe shi ba zai yi nasara.

"Abin takaici ne a zaben 2015, kuri'u miliyan 10 kacal Buhari ya samu daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

"Amma wannan karon, ina son jihar Anambra kawai ta bawa Buhari kuri'u fiye da miliyan 1."

Dan takarar mai wakiltan Arewa da Kudancin Nnewi da mazabar Ekwusigo, Injiya Jude Onyeka ya ce zaben 'yan takarar APC ne zai kawo romon demokradiyya a yankin.

A bangarensa, jigo a jam'iyyar, Cif George Muoghalu ya shawarci magoya bayan jam'iyyar kada su bari a rude su da kudi ko wani abin masarufi domin zaben wanda ba zai sama alheri a gare su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel