AIB ta binciko dalilin faduwar jirgin saman Osinbajo

AIB ta binciko dalilin faduwar jirgin saman Osinbajo

Hukumar binciken hatsari (AIB) ta saki rahoton sakamakon bincike na farko da ta gudanar dangane da hatsarin jirgin saman da ke dauke da mataimakain shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinabjo.

A farko-farkon watan nan na Fabarariru da mu ke ciki ne jirgin sama mai saukar ungulu ya fadi da Osinbajo da ‘yan tawagar sa a garin Kabba da ke jihar Kogi yayin da su ke kan hanyar su ta zuwa kamfen.

Osinbajo da ragowar tawagar mutanen da ke cikin jirgin sun tsallake rijiya da baya, sun tsira ba tare da samun ko kwarzane ba.

Caverton, kamfanin da ya mallaki jirgin, y ace hatsarin ya afku ne sakamakon rashin kyan yanayi tare da yin alkawarin gudanar da bincike.

AIB ta binciko dalilin faduwar jirgin saman Osinbajo

Jirgin saman Osinbajo da ya yi hatsari
Source: Twitter

Amma a rahoton ta, AIB ta alakanta afkuwar hatsarin da rashin gudanar da bincike a kan filin da aka shirya saukar jirgin a garin Kabba.

AIB ta bayyana cewar kamata ya yi kamfanin Caverton ya gudanar da bincike a kan yanayin filin wasan da aka tsara Osinbajo zai sauka a garin Kabba.

DUBA WANNAN: Asara: Wani mutum mai shekaru 44 ya amsa laifin yi wa yar shekara 6 fyade

Rahoton ya bayyana cewar a kan samu tashin kura da ke rage karfin ganin direba a duk lokacin da jirgi zai sauka a fili mai yawan rairayi.

Da ya ke Magana da manema labarai a yau, Laraba, a filin jirgi na Murtala Muhammed da ke Legas, kwamishinan AIB, Akin Olateru, ya ce akwai sakaci wajen kiyaye dokokin kiyaye hadurra a bangaren direban jirgin.

Olateru ya ce kamata ya yi kamfanin Caverton ya gudanar da bincike don sanin yanayin wurin da jirgin da ke dauke da Osinabajo zai sauka tun kafin tashin su zuwa jihar Kogi.

Kamfanin Caverton bai gudanar da wani bincike a kan yanayin wurin da jirgin zai sauka ba,” a cewar Olateru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel