Zabe: 'Yan takara 10 sun janye goyon bayan su ga Bindow

Zabe: 'Yan takara 10 sun janye goyon bayan su ga Bindow

'Yan takarar gwamna guda 10 da suka rattaba hannu kan yarjejeniya da Gwamna Jibrilla Bindow na Jihar Adamawa sun janye goyon bayansu daga gareshi.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa jami'yyun sune Accord Party, ANP, PPN, CAP, JMPP, MEGA Party, PPA, ZLP, YPP and NCP.

'Yan takarar a karkashin kungiyar New Generation Governorship Forum (NGGF) sun shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa sun janye goyon bayansu ne saboda Gwamna Bindow ya ki daukan shawarwarin da suka bashi na inganta aiki.

Dan takarar gwamna na jam'iyyar YPP, Simon Bawa wanda shine Kakakin NGGF ne ya bayar da sanarwar janye goyon bayansu ga Bindow.

DUBA WANNAN: Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa

Zabe: 'Yan takara 10 sun janye goyon bayan su ga Bindow

Zabe: 'Yan takara 10 sun janye goyon bayan su ga Bindow
Source: Facebook

Mr Bawa ya ce dukkansu sun fara yakin neman zabensu kuma za suyi takara a babban zaben da ke tafe.

"A halin yanzu, mun janye goyon bayan da muka bawa Gwamna Bindow da jam'iyyar APC na yin tazarce a jihar Adamawa.

"Mun fara gudanar da kamfen din mu domin neman kuri'un al'umma da zai bamu damar bawa al'umma romon demokradiya," inji shi.

A yayin da ya ke mayar da martani kan janye goyon bayan 'yan takarar gwamnan guda 10, Kwamishin watsa labarai da tsare-tsare na jihar, Ahmed Sajoh ya ce son kai ne yasa 'yan takarar daukan wannan matakin.

Ya ce ba za su iya aiki tare da Gwamna Bindow ba saboda shi ya mayar da hankali ne wurin samar da ayyukan cigaba da al'ummar Adamawa a maimakon 'farantawa wasu tsiraru rai'.

NAN ta ruwaito cewa jam'iyyun siyasa 29 ne za su tsayar da 'yan takarar Gwamna a jihar ta Adamawa a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel