2019: Malaman Makaranta sun ba Shugaba Buhari goyon bayan su

2019: Malaman Makaranta sun ba Shugaba Buhari goyon bayan su

- Wasu Malamai a Najeriya sun yi kira ga jama’a su zabi Buhari

- Wadannan Malamai sun ce Buhari ya cancanci ya zarce a 2019

- Wannan kungiyar yace Shugaban kasar ya dauko hanyar gyara

2019: Malaman Makaranta sun ba Shugaba Buhari goyon bayan su

Wasu Malaman Makaranta sun ce Buhari ya cancanci ya zarce
Source: Facebook

Mun ji labari cewa wasu Malamai da ke koyarwa a makarantun jami’o’i da makarantun gaba da sakandare da kwalejin ilmi a Najeriya sun nuna goyon bayan su ga tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Jaridar The Sun ta rahoto mana cewa malaman da ke aiki a manyan jami’o’i da makarantu da kuma kwaleji sun nemi Mabiyan su, su zabi Buhari a karo na biyu. Shugaban wannan kungiya, Farfesa Bolarinwa Bolaji, ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Kiristocin Arewa sun bi Atiku yayin da wasu su ka bi layin Buhari

A jiya ne wannan kungiya ta Malaman kasar tayi wani taro a babban birnin tarayya Abuja, inda ta cin ma matsaya cewa za su marawa shugaban kasa Buhari baya ne ya zarce a kan mulki domin ya cigaba da kokarin da yake yi ba gyara kasa.

Bolarinwa Bolaji, ya nemi mutanen Najeriya gaba daya su ba gwamnatin Buhari dama ta sake komawa kan mulki domin yakar cin hanci da rashawa tare da inganta tattalin arziki da kuma kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita.

Shugaban wannan kungiya ta malamai yake cewa shugaba Buhari ya karbi kasar ne a wani irin yanayi na sukurkucewa da kuma mugun banbanci na addini da kuma kabilanci don haka yake ganin akwai bukatar ya zarce don yayi gyara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel