Hukumar zabe na yiwa PDP aiki - Oshiomhole

Hukumar zabe na yiwa PDP aiki - Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressive Congress yayi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta na yiwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) aiki.

Adams Oshiomhole, ya bayyanawa manema labarai hakan ne a yau Laraba a birnin tarayya Abuja, inda ya ce; hana jam’iyyar ayyana dan takara a jihohin Ribas da Zamfara da hukumar INEC din ta yi, ya sa su sanya alamar tambaya akan hukumar ta INEC din, kuma hakan ya sanya su damuwa.

Ya kara da cewa: “hukumar zabe mai zaman kanta ta nuna rashin adalci akan jam’iyyar APC. Da alama hukuman na yiwa jam’iyyar PDP aiki."

Hukumar zabe na yiwa PDP aiki - Oshiomhole

Hukumar zabe na yiwa PDP aiki - Oshiomhole
Source: Depositphotos

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata kotun daukaka kara da ke jihar Sokoto ta warware hukuncin da wata babbar kotu a jihar Zamfara ta yanke a kan hana hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) karbar sunayen ‘yan takarar jam’iyyar APC na kujeru daban-daban a zaben da za a yi cikin watan Fabarairu da Maris.

Hukuncin kotun ya share wa jam’iyyar APC hanyar shiga domin a fafata da ita a dukkan zabukan shekarar nan da za a fara ranar Asabar mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta fi kowace jam'iyya muhimmanci – Buhari

Kotun mai alkalai uku ta yi warware hukuncin kotun farkon ne biyo bayan janye karar da Aminu Jaji, wanda ya shigar, ya yi.

INEC ta kafe kan cewar ba zata karbi sunayen ‘yan takarar APC daga jihar Zamfara ba saboda gaza kammala zabukan cikin gida a kan lokaci da jam’iyyar ta yi. Hukumar zaben ta tsaya tsayin daka a kan matakin da ta dauka bayan wasu hukunci ma su cin karo da juna da kotun jihar Zamfara da wata ta tarayya su ka zartar a rana guda.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel