Harin Boko Haram kan gwamnan Borno: Soja 1, mutane biyu sun rasa rayukansu, Shettima na nan lafiya

Harin Boko Haram kan gwamnan Borno: Soja 1, mutane biyu sun rasa rayukansu, Shettima na nan lafiya

Jami'in soja daya, masu farar huka biyu suna rasa rayukansu a ranan Laraba yayinda yan Boko Haram suka budewa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wuta a yankin Borno ta Arewa yayinda yaje yakin neman zabe.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da hakan ga jaridar The Nation. Ya ce an yan ta'addan sun kai farmakin ne a Gajibo, karamar hukuma Dikwa na jihar Borno.

Majiyar ta bayyana cewa Shettima ya tsira ba tare da wani rauni ba saboda harin ya shafi motocin da ke bayansa ne.

Yace: "Abin takaici ne yan Boko Haram sun yi amfani da daman tsawon motocin gwamnan. Lokacin da abinda ya faru, gwamnan ya riga ya wuce."

"Mutane uku sun rasa rayukansu- soja daya da masu farar huka biyu. Yanzu muke dawowa daga Maiduguri."

Bayan kwanaki kadan, Wasu mambobin kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun kai mumunan harin Bom wata masallaci a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ranan Asabar, 16 ga watan Febrairu, 2019, akalla mutane 11 sun rasa rayukansu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Borno, Damien Chukwu, ya tabbatar da hakan inda yace hakan ya faru ne misalin karfe 5:40 na asuba.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel