2019: Darektan Kamfen na APC Monday Aighobahi ya fada hannun Miyagu

2019: Darektan Kamfen na APC Monday Aighobahi ya fada hannun Miyagu

- ‘Yan bindiga sun sace wani Darektan yakin neman zaben APC

- Wadannan Miyagun Mutane sun yi gaba da mutumin ne a jiya

- Monday Aighobahi yana cikin manyan jagorori na APC a Edo

2019: Darektan Kamfen na APC Monday Aighobahi ya fada hannun Miyagu

An sace Darektan yakin neman zaben wani 'dan majalisar Edo
Source: UGC

Labari ya zo mana cewa wasu ‘Yan bindiga da ba a san su ba, sun sace wani Darektan yakin neman zabe na Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Edo. An sace Monday Aighobahi ne a jiya Ranar Talata a lokacin yana yawon kamfe.

Kamar yadda labari ya iso mana, ‘yan bindigan sun sace Monday Aighobahi ne a Garin Ofosu da ke cikin gundumar Ogbogui da ke jihar Edo. Aighobahi yana cikin manyan kusoshin APC a jihar ta Edo da ke kudancin Najeriya.

Yanzu haka wannan Bawan Allah da aka rasa inda yake, shi ne shugaban kamfe na ‘dan takarar kujerar ‘dan majalisar tarayya na mazabar Ovia watau Dennis Idahosa. Idahosa tsohon shugaban karamar hukuma ne na yankin.

KU KARANTA: An sheka asibiti bayan wasu Mabiyan APC da PDP sun ba hammata iska

Wadanda su ka san yadda abin ya faru, sun bayyana cewa an sace Aighobahi ne bayan wani taron gangami da APC ta shirya a garin Ofosu inda yake kokarin kira ga mutanen mazabar su zabi Dennis Idahosa a zaben da za ayi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo watau Hakeem Odumosun,ya bayyana cewa har yanzu bai samu wani cikakken bayani game da wannan abin takaici. An dais aba fama da rikici da bangar siyasa a wannan yanki na Ofosu.

Manyan jam’iyyar APC mai mulki sun yi kira ga Mabiyan su cewa su kwantar da hankalin su inda su ke sa rai cewa za a fito da Mista Monday Aighobahi daga duk inda aka tsare sa ba tare da bata lokaci ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel