Yan bindiga sun kaiwa shugaban kamfen Buhari mumunan hari

Yan bindiga sun kaiwa shugaban kamfen Buhari mumunan hari

Da safiyar Laraba ne wasu yan bindiga suka budewa motar shugaban kungiyar kamfen Buhari wato BCO ta kasa, Danladi Garba Pasali, mumunan wuta.

Yayinda yake bayani ga jaridar Daily Nigerian, Danladi Pasali ya bayyana cewa yan bindigan sun bude musu wuta ne yayinda suke hanyar dawowa da taron jigogn yakin neman zaben shugaban kasa da akayi ranan Talata a Abuja.

Ya kara da cewa shi da direbansa sun jikkata kuma suna jinya a asibitin Rayfield Medical Center dake Jos, jihar Plateau.

Yace: "Na bar Abuja da safen nan domin kaddamar da ofishin BCO dake gidan Korinjo kawai sai wasu yan bindiga suka taremu misalin karfe 6."

Sun bude musu wuta ne a karamar hukumar Akwanga dake jihar Nasarawa.

A bangare guda, Babba kotun jihar Flato ta baiwa wasu mutane bakwai da ake zargi da kisan marigayi Janar Ibrahim Alkali beli.

An gurfanar da su ne da laifin hannu cikin kisan tsohon shugaban gudanarwa hukumar sojin Najeriya, wanda aka hallaka a hanyarsa daga Abuja zuwa Bauchi. Za ku tuna cewa a watan Disamban 2018, kotu ta sake wasu daga cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel