Najeriya ta fi kowace jam'iyya muhimmanci – Buhari

Najeriya ta fi kowace jam'iyya muhimmanci – Buhari

A daidai lokacin da ake shirin shiga ranakun zabe nan da kwanaki uku, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa kasar Najeriya ta fi kowace jam’iyya muhimmanci.

Buhari wanda ke neman tazarce a zabe mai zuwa karkashin inuwar jam’iyyar APC, ya bayyana wannan ra’ayin ne a ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairu lokacin da ya ke jawabi wurin taron rattaba hannu a yarjejeniya karshe kafin zaben 2019, a Babbar Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Abuja.

Buhari ya ce wannan zabe mai zuwa na da muhimmaci matuka da gaske ga kasar nan da kuma kafuwar dimokradiyyar kasar.

Najeriya ta fi kowace jam'iyya muhimmanci – Buhari

Najeriya ta fi kowace jam'iyya muhimmanci – Buhari
Source: Depositphotos

Ya ce jama’a da dama sun dora idanun su domin ganin cewa an gudanar da zabe sahihi kuma karbabbe, kuma duk da irin shirin da masu gudanar da zabe suka yi, ba za a rasa cimma kabubale ba.

Ya ce abu na biyu dangane da zaben shi ne wannan mai zuwa zai zo bayan na 2015 da aka gudanar, wanda kowa ya tabbatar da cewa sahihin zabe ne aka gudanar.

Shugaban ya kara da cewa abu na uku shi ne ganin yadda matasa suka yi ambaliyar shiga wannan zabe, saboda shrin ‘Not Too Young To Run da aka shigo da shi.

KU KARANTA KUMA: Duk zance ne, nine kadai na ke da masaniyar waye zai lashe zaben shugaban kasa - Guru Maharaj

Akwai kuma tumbatsar yawan jam’iyyu da aka yi wannan zaben, wanda ba a taba samun yawan jam’iyyu kamar wannan zaben ba.

Daga nan sai ya yi kiran da kowa ya bada tasa gudummawa domin tabbatar da samun nasarar zaben, ya na mai cewa Najeriya ta fi kowace jam’iyyar siyasa muhimmaci.

Buhari ya kara da cewa sai da ya tabbatar INEC ta samu dukkan kayann aikin da ta ke bukata. Ya kuma yi addu’ar Allah ya sa a gudanar da zabe lafiya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairu a Abuja ya roki yan takarar Shugaban kasa a zaben ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu da su bi hikimomin da ke tattare da shiga yarjejeniyar zaman lafiya domin ayi zabe cikin lumana.

Shugaba Buhari yayi wannan rokon ne a lokacin da shi da sauran yan takarar Shugaban kasa ciki harda tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar suka hadu a wajen sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel